Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-18 12:10:04    
Nijeriya ta mika tsibirin Bakassi ga Kamaru

cri

A ran 14 ga wata,Nijeriya ta mika tsibirin Bakassi ga kasar Kamaru,daga nan aka sa aya ga gardamar da ta shafe shekaru da dama da aka yi ta yi tsakanin kasashen nan biyu.Babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bayyana cewa muhimmin al'amari ne a duniya,Nijeriya ta zama abin koyi ga sauran kasashe da yankuna na duniya wajen warware gardama kan yankuna. Duk da haka gwamnatin Nijeriya ta fuskanci matsin lamba daga kafofin yada labarai na gida sabo da mika tsibirin Bakassi,shi ya sa tana nan tana sha jarrabawa bayan mikawa.

Tsibirin Bakassi yana bakin kudu na tsakanin Nijeriya da Kamaru,fadinsa ya kai muraba'in kilomita dubu,yana da arzukin man fetur da gas.Gwagwarmar da ake yi tsakanin Kamaru da Nijeriya ba ta daina ba domin mallakar wannan tsibirin,har ma aka yi tashin hankali na zubar da jinni. A shekara ta 1994, Kamaru ta gabatar da batun mallakar tsibirin Bakassi ga kotun duniya ta Hague. A watan Oktoba na shekara ta 2002,kotun duniya ta Hague ta tsaida kudurin mayar da tsibirin Bakassi ga Kamaru. Bisa kudurin nan,gwamnatocin kasashen biyu sun daddale yarjejeniyar Green Tree a birnin New York na kasar Amurka a ran 14 ga watan Augusta na shekara ta 2006,daga nan an fara gudanar da shirin mika tsibirin Bakassi.

Duk da haka,bisa abubuwan da aka tanada a cikin tsarin mulkin kasa na Nijeriya,an bayyana cewa dole ne kowace yarjejeniya da gwamatin Tarayyar Nijeriya ta daddale da kowace kasa ta sami amincewa daga majalisun dokokin kasa,in ba haka ba ba ta iya fara aiki. A watan Nuwanba na shekara ta 2007,majalisun dokoki na Nijeriya sun yanke shawara cewa yarjejeniyar Green Tree ba ta da amfani bisa dokokin kasa, sabili da haka Nijeriya ba ta iya mayar da tsibirin Bakassi ba. Ko ma a yan kwanakin gabannin bikin mikawa, kotun Tarrayar Nijeriya a birnin Abuja ta bayar da umurni ga gwamnatin Nijeriya da ta kiyaye halin da ake ciki yanzu a tsibirin Bakassi.A sa'I daya,yawancin mutanen Nijeriya suna masus ra'ayi cewa mika tsibiri ya bayyana cewa gwamnatin Nijeriya ba ta da karfi domin babu wata kasa a duniya da ta kama gaba ta mika yankinta. Kwanakin baya,wasu kungiyoyin fafitika na Nijeriya sun sha kai hari kan sojojin Kamaru a yankin dab da tsibirin Bakassi. Kuma sun kankama da cewa idan aka mika tsibirin tare da nasara,za su kai Karin hari kan sojojin Kamaru.

Kan matsin lamba mai karfi,gwamnatin Nijeriya ta sha nanata cewa za ta bi kudurin kotun Duniya kan tsirin bakassi,a kwanaki biyu kafin bikin,kakakin shugaban kasa Umaru Yar'adua na Nijeriya ya sha gaya wa kafofin yada labarai cewa kamar yadda yawanncin mutanen Nijeriya,mika tsibirin Bakassi wani batu ne mai bacin rai sosai ga shugaban kasa, amma ya kamata Nijeriya ta cika alkawarin da ta dauka ga sauran kasashen duniya. Shugaba Yar Adua ya kuma ba da umurni ga ministan shari'a da ya duki dukkan matakan da suka wajaba domin kawar da kudurin kotun da abin ya shafa. Domin tabbatar da gudanar da biki lami lafiya da gudun tashin hankula,Nijeriya ta tura sojoji da 'yan sanda da yawa domin gadin wurin yin bikin mikawa.

Masu binciken al'amura suna masu ra'ayi cewa wani muhimmin dalili da ya sa Nijeriya ta mika tsibirin Bakassi ga Kamaru shi ne a kan matsayin babbar kasa a Afrika,Nijeriya tana dokin taka Karin muhimmiyar rawa a cikin harkokin duniya da na nahiyoyi, musamman a kwanan baya, Nijeriya ta gabatar da bukatunta na zama zaunanniyar wakiliya a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya.sabo da haka da yake batun ya saba wa burin jama'a,gwamnatin Nijeriya ta ga kamata ya yi ta bi kudurin kotun duniya domin kafa kyakyawan misalign koyo ga sauran kasashen duniya.

1 2