To, a gaskiya 'yan baitocin sun burge mu sosai da sosai, kuma muna yi wa dukan mambobin kungiyar Jeyrala godiya, sabo da goyon bayan da kuka ba mu, mun gode. Allah ya saka da alheri.
Bayan wannan, wasu masu sauraro sun kuma rubuto mana shawarwarinsu dangane da shirye-shiryenmu a lokacin wasannin Olympics. Kamar yadda ya rubuta a cikin wasikarsa, Idris Dagalan ya ce, "Game da gasar Olympic ta bana, na fi son samun bayanai akan wasan gudu na mata da maza,wasan kwallon kafa,wasan laun-tainis da kuma wasan kwallon kwando."
Sa'an nan, malami Yusuf ya rubuto mana cewa, "Madallah da matsowar wannan gasar.wasannin da kowa yake da burin yaji bai wuce wasanni da duk Duniya ta raja'a a kai ba, wato kwallon kafa. Zai yiwu jama'a su dinga son su ji tarihin 'yan wasan.cikin bayanin ko wane wasanni da yake cikin afkuwa a wannan lokacin."
To, mun gode muku da ba mu shawarwarin, kuma za mu yi kokarin biyan bukatunku, muma kuma fatan za ku dinga kasancewa tare da sashen Hausa na rediyon kasar Sin a lokacin wasannin Olympics.
Masu sauraro, "duniya daya, mafarki daya". An fara wasannin Olympics a nan birnin Beijing, kuma 'yan wasa da jama'a sun taru a nan birnin Beijing domin wasannin Olympics, domin mafarkinsu daya na Olympics. Beijing a shirye take, kuma tana maraba da zuwan aminai daga kasashen duniya daban daban.(Lubabatu) 1 2 3 4
|