Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-15 15:26:35    
Sakonnin masu sauraro a kan wasannin Olympics na Beijing

cri

An bude wasannin Olympics a nan birnin Beijing, kuma yanzu duk duniya na zura ido ga birnin Beijing da kuma kasar Sin. Masu sauraronmu ma suna sa rai sosai a kan wasannin Olympics na Beijing, kuma kwanan nan, sun rubuto mana sakonni da yawa, don nuna goyon baya da fatan alheri ga wasannin Olympics na Beijing.

Mamane Ada, wanda ya zo daga birnin Yamai, jamhuriyar Nijer, ya rubuto mana cewa, "kamar yadda hankalin kasashen duniya ya karkata zuwa kasar Sin, to haka ne su ma 'yan Nijar suke alfahari da wannan wasanni na kasa da kasa. Ganin cewa kasar Nijar za ta halarci wannan konbala a fannoni daban daban ne, ya sa al'umar Nijar take fatan kasar Sin za ta cimma burinta wajen shirya wannan wasanni cikin lumana da jin dadin kowa. Masu sauraren cri dake nan birnin Yamai muna kira da cewa, a lokacin wannan wasanni, ku rika bada labaru kan 'yan wasan Nijar dake cikin wannan konbala."

To, madallah, Mamane Ada, muna maka godiya da rubuto mana wannan wasika, ba shakka, a lokacin wasannin Olympics, za mu mai da hankali sosai a kan 'yan wasan kasashen Afirka, ciki har da Nijer, kuma za mu dinga ba da labarai a kansu, da fatan za ku kasance tare da mu a kullum, don ku dinga samun labaran 'yan wasan Nijer. Bayan haka, muna kuma fatan 'yan wasan Nijer za su cimma burinsu a gun wasannin Olympics na Beijing.

Sa'an nan, Mohammed Idi Gargajiya, shugaban kungiyar masu sauraron CRI da ke jihar Gombe, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa,

"A matsayinmu na abokan jama'ar kasar Sin baki daya, ko shakka babu muna jin murna da farin ciki kwarai da gaske game da gasar wasannin olympic ta Beijing 2008. Sabo da haka, yanzu dukkan hankulanmu sun karkata ne kacokam kan birnin Beijing. Lallai ba shakka a ganinmu birnin Beijing ya cika dukkan alkawuran da ya dauka na shirya gasar wasannin olympic Beijing 2008.

Ban da wannan kuma, abin farin ciki shi ne birnin Beijing ya kara tsaftacewa da mutuntawa da kuma darajanta wasannin olympic ta dukkan fannoni daban daban, ba ga yan wasa kawai ba, harma ga dukkan al'ummar duniya baki daya.

Daga karshe muna fatan Beijing zai samu cikakkiyar nasara wajen gudanar da wannan gaggarumin biki mafi ban sha'awa da ban mamaki da kuma ban al-ajabi, sa'annan kasar Sin tana da nasara kuma za ta yi nasara a gun gasar wasannin olympic ta Beijing 2008 wajen samun lambobin yabo na zinariya mai daraja."


1 2 3 4