Dalili na biyu shi ne, an saki Mr. Waghf ne saboda tasiri kalilan ne yake da shi, wanda ba zai haifarda tsaiko ga yadda ake sarrafa halin da ake ciki yanzu a wannan kasa ba.
Jama'a, ra'ayoyin bainal jama'a sun kuma yi hasashen cewa, a yanzu haka dai, batun lokaci ne kawai da ake la'akari da shi kan yaushe ne zai saki shugaba Sidi Abdallahi na kasar sakamakon babban matsi daga ketare, amma duk da haka, makomar Abdallahi tana kasa tana dabo in har ya sake dawowa kan dandalin siyasa na kasar.
Da farko, ana ganin cewa, bangaren soji da ya yi juyin mulki ya rigaya ya sarrafa yanayin siyasa na kasar, akwai alamun dake shaida cewa, an riga an dakushe ikon mulkin da shugaba Abdallahi yake da shi; Ban da wannan kuma, jim kadan bayan da aka yi juyin mulkin, bangaren soji ya bayar da wata sanarwa cewa, za a gudanar da zaben shugaban kasa cikin 'yanci kuma bare da rufa-rufa ba nan da gajeren lokaci gwargwadon iyawa, ta yadda za a bada tabbaci ga aiwatar da harkokin mulkin gwamnatin kasar iri daban-daban lami-lafiya daidai bisa abubuwan da aka tanada cikin tsarin kundin mulkin kasar. Hakan shi ma ya shaida cewa, akwai yiwuwar dakatar da rayuwar siyasa ta shugaba Abdallahi tun daga wanna lokaci.
Amma kuwa, wassu mutane masu kallon lamuran yau da kullum sun ce, har ila yau, bangaren soji da ya yi juyin mulki na Mauritania na fuskantar babban kalubale yayin da yake kokarin gudanar da yakin neman zabe a kasar lami-lafiya da maido da oda da kuma kundin tsarin mulkin kasar:
Da farko, wassu kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sun rigaya sun bayyana a fili cewa, sun nuna rashin amincewa da yin zaban shugaban kasar daga gefe daya kurum; Ban da wannan kuma, idan ba a gudanar da zaben cikin gajeren lokaci ba, to watakila kwamitin harkokin kasar zai tafiyar da harkokin gwamnati cikin dogon lokaci har zuwa ranar da za a yi zaban shugaban kasar. Saboda haka ne, ake shakkar cewa ko gwamnatin da sojoji ke jagoranta za ta iya daidaita matsalolin da take fuskanta ko a'a. ( Sani Wang ) 1 2
|