Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-13 17:14:40    
Ina ne halin da ake ciki a Mauritaniya yake zuwa

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, shekaranjiya dai, bangaren soja da ya yi juyin mulki a kasar Mauritaniya ya sako firaministan gwamnatin kasar Yahya Ahmed Waghf da ake tsare da shi. Kuma jiya dai, "kwamitin harkokin kasa" da bangaren soji ke jagoranta ya zartar da wata dokar shari'a don danka wa jagoran dakarun da suka yi juyin mulki nauyin nada firayiminista da kuma saruan kusoshin gwamnatin kasar. Wassu manazarta sun yi hasashen cewa, wassu alamun cigaban halin da ake ciki a kasar Mauritaniya sun shaida cewa, bangaren soji da ya yi juyin mulkin ya rigaya ya sarrafa halin da ake ciki yanzu a kasar yayin da yake kokarin sassanta babban matsin da gamayyar kasa da kasa ke yi masa.

Ra'ayoyin bainal jama'a sun dauka cewa, dalilai biyu ne da bangaren soji da ya yi juyin mulkin ya saki Mista Wafhf. Dalili na farko shi ne, domin sassanta babban karfin matsi da gamayyar kasa da kasa ke yi masa. Juyin mulkin soji da aka yi a kasar Mauritaniya ya janyo kakkausar suka daga gamayyar kasa da kasa; Kazalika, kasashen Amurka da Fransa sun dakatar da bai wa Mauritaniya tallafi daya bayan daya; bugu da kari, kungiyar tarayyar Turai ta ce, juyin mulkin sojin zai yi barazanar dakatar da ba wa Mauritaniya tallafin da ya kai dolar Amurkia miliyan dari biyu da arba'in da daya nan da shekaru biyar masu zuwa bisa yarjejeniyar da aka daddale tsakanin kungiyar tarayyar Turai da Mauritaniya; Dadin dadawa, kungiyar tarayyar Afrika ita ma ta yi shelar dakatar da ikon wakilcin Mauritaniya a cikin kungiyar AU. Hakan ya sa bangaren soji da ya yi juyin mulki shiga cikin halin kaka-ni-ka-yi.


1 2