Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-13 15:09:44    
Yawan masu yawon shakatawa a kasar Sin zai karu cikin sauri bayan gasar Olympic

cri

A cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, sana'ar yawon shakatawa ta riga ta zama wata muhimmiyar sana'a ga tattalin arzikin kasar Sin. Yanzu jimlar kudaden da aka samu a fannin sana'ar yawon shakatawa ta kai kashi 4 cikin kashi dari bisa na duk jimlar kudaden samar da kayayyaki na kasar Sin. Bisa kididdigar da aka yi, yawan masu yawon shakatawa na kasashen waje da suka zo kasar Sin a shekara ta 2007 ya kai miliyan 132, sabo da haka, yanzu kasar Sin tana matsayi na 4 a duk duniya wajen sana'ar yawon shakatawa. Yanzu a matsayin mai masaukin gasar Olympic ta karo na 29 na lokacin zafi, kasar Sin ta riga ta zama wurin yawon shakatawa da dimbin masu yawon shakatawa na kasashen waje suka tabbata za su zo. Tabbas ne, sana'ar yawon shakatawa za ta samu cigaba cikin sauri sosai.

A gun wani taron manema labaru da aka yi a cibiyar watsa labaru ta kasa da kasa ta Beijing, wato BIMC a ran 12 ga wata, Mr. Wang Zhifa, mataimakin shugaban hukumar yawon shakatawa ta kasar Sin ya ce, ko da yake yawan masu yawon shakatawa da suka zo daga kasashen waje ya samu karuwa cikin sauri a lokacin gasar Olympic, amma har yanzu bai kai matsayin koli ba tukuna. An bayyana cewa, tsarin masu yawon shakatawa da suke zuwa kasar Sin ya samu canji sakamakon gasar Olympic. A tsakanin watan Janairu zuwa watan Yuli, galibin masu yawon shakatawa da suka zo kasar Sin masu yawon shakatawa ne na yau da kullum. Amma bayan an shiga watan Agusta, yawan masu yawon shakatawa na yau da kullum ya ragu, yawan masu halartar gasar da 'yan kallon gasar ya karu sosai.


1 2 3