A cikin kyakkaywan wurin yawon shakatawa na Chaoyang da ke nan birnin Beijing, akwai wani karamin tsibiri a tsakiyar tabki. A kansa kuma, an shimfida rairayi. Wato shi ne filin wasan kwallon raga na rairayin bakin teku da za a yi amfani da shi a gun taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar gobe.
Filin wasan kwallon raga na rairayin bakin teku da ke wurin yawon shakatawa na Chaoyang na Beijing na matsayin filin wasa na wucin gadi domin taron wasannin Olympic. Ya hada da babban filin wasa guda daya da filayen wasan dumamar jiki guda 2 da kuma filayen wasa na horo guda 6. An samar da kujeru dubu 12 ga 'yan kallo. Kuma an shimfida rairayi mai nauyin ton dubu 17 ko fiye a cikin wannan filin wasan kwallon raga, wadanda aka yi jigilarsu daga bakin teku na tsibirin Hainandao na kasar Sin kai tsaye, a maimakon a kawo daga kasashen ketare. An fara gina wannan filin wasa a watan Disamba na shekarar 2005, aikin ginawa ya kawo karshe a watan Yuni na shekarar da muke ciki.
1 2
|