Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-08 15:13:23    
Duk domin duniyarmu da kuma burinmu gaba daya

cri

Yau, wato ranar 8 ga watan Agusta na shekarar 2008, wata rana ce ta musamman ga Beijing da kuma kasar Sin gaba daya, wato ke nan a yau ne aka yi bikin bude gasar wasannin Olympics ta 29, inda 'yan wasa, da masu koyar da 'yan wasa da kuma gaggan baki daga kasashe da yankuna daban-daban na duniya suka hadu a wuri daya a karkashin tutar Olympics mai zobba biyar domin more wasanni da kuma mika sakonnin zaman lafiya da sada zumunci da kuma rera wakar dake da babban take kamar haka: "Duniya kuma buri daya". " lallai kirarin ' Duniya daya kuma buri daya' ya bayyana hasashen Olympics da kuma makasudin gasar wasannin Olympics ta Beijing. Wannan kirari ya bayyana sahihin burinmu, wato ke nan jama'ar kasar Sin suna so su sanya kokari matuka tare da jama'ar duk duniya wajen kara yin musanye-musanye da hadin gwiwa don rubuta sabon shafin wasannin Olympics na kasa da kasa, ta yadda za a kirkiro kyakkyawar makoma ta bil adama".

Aminai 'yan Afrika, kamar yadda suka san cewa, cikin shekaru sama da 100 da suka gabata bayan da aka kafa gasar wasannin Olympics ta zamanin yau, ko da yake har wa yau dai ana yin yake-yake da kai hare-hare da kuma yin barazanar ta'addanci a duk duniya, amma ko kusa dukkan 'yan adam ba su yi watsi da burinsu na samun zaman lafiya da jituwa ba duk da lokuta masu bakanta ransu da suka samu. Daidai bisa kirarin gaskiya na " Duniya daya kuma buri daya" ne, mutane masu banbancin launin fata a kabilu wadanda suke yin amfani da harsuna daban-daban suka zo nan Beijing daga wurare daban-daban na duniya da zummar cimma babban burinsu." Taya wa kasar Sin murna! Taya wa Beijing murna! Gasar wasannin Olympics, wani gagarumin taro ne irin na kasa da kasa. Na taya wa kasar Sin murnar samun wannan kyakkyawar damar gudanar da gasar wasannin Olympics".

Mista kalonzo Musyoka, mataimakin shugaban kasar Kenya shi ne ya fadi hakan kafin ya tashi zuwa birnin Beijing don kallon bikin bude gasar wasannin.

An kiyasta cewa, gasar wasannin Olympics ta Beijing ta samu halarcin shugabanni fiye da 80 na kasashe da na gwamnatoci da kuma tawagogin 'yan wasa 205, wanda ba safai akan ga irinsa ba a tarihi.

1 2