Tun daga watan Mayu na shekarar da muke ciki, an soma kara tsanantawar sabane-sabane a tsakanin shugaba, da gwamnati, da kuma 'yan hamayya na majalisar dokoki. A ranar 16 ga watan Yuli, Mr. Abdallahi ya bayar da umurnin shugaba, inda ya yi shelar kafa sabuwar gwamnatin kasar Mauritania. Ban da firayin minista kuma, sabuwar gwamnatin ta kunshi mambobi 30, dukkansu sun fito daga kungiyar kawancen duk kasar ta dimokuradiya da bunkasuwa, wadda ke karkashin shugabancin firayin ministan kasar Mr. Waghf.
A ranar 6 ga wata, gidan rediyon kasar Mauritania, da gidan talibijin na kasar sun sake watsa shirye-shiryensu. Bayan haka kuma, daya bayan daya Janar Aziz, wanda ya yi juyin mulkin soja ya gana da jakadun kasashen Faransa, da na Amurka, da kuma na sauran kasashe da ke kasar Mauritania. Wasu jam'iyyu na kasar Mauritania su ma sun bayar da sanarwa cewa, a hakika dai suna adawa da juyin mulkin da wasu sojoji suka yi, sun jaddada cewa, wannan zai kawo tasiri ga zaman karko na kasar.
Bayan da aka yi juyin mulkin soja a kasar Mauritania, kasashen duniya sun yi allah wadai da lamarin, ciki har da babban sakataren M.D.D. Ban Ki-Moon, da kungiyar AU, da shugaban kasar Nijeriya Umaru Musa 'yar Adua.
1 2
|