Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-07 16:17:51    
An yi juyin mulkin soja a kasar Mauritania

cri

A ranar 6 ga wata da safe, sojojin kasar Mauritania sun yi juyin mulkin soja, a sakamakon haka, sun mamaye fadar firayin minist, da ta shugaban kasar da ke cibiyar birnin NouaKchott, wato babban birnin kasar, bayan haka kuma, sun kama shugaba Sidi Ould Cheikh Abdallahi na kasar, da kuma firayin ministan kasar Yahya Ould Ahmed Waghf.A wannan rana da sassafe, Mr. Abdallahi ya sa hannu a kan umurnin shugaban kasar, inda ya yi shelar sauke janar-janar uku, da kanar daya daga mukamansu, wadanda suka kunshi Mr. Mohamed Ould Abdel Aziz da ke kula da hedkwatar musamman ta ba da shawara ga shugaban kasar, da hafsan-hafsoshin rundunar soja Ould Cheikh Mohamed Ahmed, da dai sauransu. Daga baya kuma, babban janar Aziz da aka sauke shi daga mukaminsa ya shugabanci rundunar tsaron shugaba shiga fadar firayin minista, da ta shugaban kasar, don yin juyin mulkin soja, har ma sun kama firayin minista, da shugaban kasar. Bayan haka kuma, an yi shelar kafa sabuwar gwamnatin da ke karkashin shugabancin Aziz. A waje daya kuma, sojojin da suka yi juyin mulkin sun sarrafa gidan rediyo, da gidan talibijin kasar, kuma sun katse shirye-shirye.

Kakakin fadar shugaban kasar Mauritaniya Abdoulaye Mamadouba ya bayar da sanarwa bayan juyin mulkin, inda ya yi zargin cewa, wannan ne juyin mulki bisa shiri da masu adawa da shugaban kasar ya sauke su daga mukamansu suka yi. Ya bayyana cewa, shugaban kasar shugaban koli ne na rundunar soja, saboda haka, kudurin da ya tsaida game da sauke janar-janar da kanar guda hudu daga mukaminsu, bai wuce ikonsa ba. Bisa labarin da muka samu an ce, dalilin da ya sa shugaba Abdallahi ya sauke wadannan jana-janar da kanar hudu daga mukaminsu shi ne, domin sun nuna goyon baya ga 'yan majalisar dokoki masu adawa, wadanda suka janye jiki daga jam'iyyar da ke rike da ragamar mulkin kasar. Kafin wannan kuma, 'yan majalisu daga majalisar dokoki da ta dattijai ta kasar Mauritania, wadanda yawansu ya kai 48 sun janye daga jam'iyyar da ke rike da ragamar mulkin kasar, saboda ba su amince da halin siyasa da ake ciki ba.

An taba yin juyin mulkin soja sau da yawa a kasar Mauritania tun bayan da kasar ta samun 'yancin kai a shekarar 1960. A ranar 3 ga watan Agusta na shekarar 2005, sojojin kasar Mauritania sun tada juyin mulki, kuma sun kafa 'Kwamitin aikin soja na dimokuradiya da adalci', a madadin mulkin Taya, wadda ya rike da mulkin kasar har shekaru 21. A watan Maris na shekarar 2007, an shirya zaben shugaban kasar Mauritania, 'dan takara mai zaman kansa Abdallahi ya samu nasara a zaben, kuma ya zama sabon shugaban kasar.

1 2