Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-06 20:35:29    
Wutar gasar wasannin Olympics ta kunna hasken zuci domin more mafarki guda

cri

Ban da wannan kuma ta hanyar mika wutar, duniya ta gano hasken zuci na kasar Sin wadda ke daukar nauyin mai masaukin wasannin Olympics, da kuma kudurin kasar Sin wajen cika alkawari. A ran 8 ga watan Mayu na shekara ta 2008, wutar gasar wasannin Olympics ta isa kololuwar tsaunin Qomolangma, dutse mafi tsayi a duniya. Wang Yongfeng, mai rike da wutar kuma shugaban hawan dutse na kasar Sin ya bayyana cewa,

"Tabbas ne dukkan mutane za su tuna da aikin mika wutar a kololuwar tsaunin Qomolangma a cikin dukkan ayyukan mika wutar wasannin Olympics na nan gaba. Har ma shi ne wani abu mai daraja sosai a cikin dukkan tarihin wasannin Olympics."

A ran 6 ga wata da karfe 8 da safe, an kaddamar da mika wutar a birnin Beijing, Yang Liwei, mutumin farko na aikin tafiyar da kumbo na kasar Sin ya zama mutumin farko da ke rike da wutar. Za a shafe kwanaki uku ana mika wutar a Beijing. Bayan da mutum na karshe da ke rike da wutar ya kunna wutar da ke cikin filin wasannin motsa jiki na kasar Sin wato "shekar tsuntsu" a ran 8 ga wata da dare, za a dasa kyakkyawar aya ga wannan aikin mika wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing wanda ya kwashe lokuta mafi yawa da shafe mutane da kuma fannoni mafi yawa a tarihi. A waje daya kuma, wannan ya shaida cewa, an kaddamar da gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekara ta 2008 a hukunce.(Kande Gao)


1 2