Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-06 20:35:29    
Wutar gasar wasannin Olympics ta kunna hasken zuci domin more mafarki guda

cri

A ran 6 ga wata, wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekara ta 2008 ta iso birnin Beijing inda za a shirya gasar bayan da aka mika ta a birane 19 na nahiyoyi 5 da kuma birane fiye da 100 na kasar Sin. Mika wutar gasar wasannin Olympics ta yada ruhun Olympics, da kara cudanya da fahimtar da ke tsakanin Sin da duniya, da kuma taimaka wa fararen hula na kasashen da aka mika wutar a ciki wajen cimma burinsu na sa hannu a cikin wasannin Olympics. To yanzu ga cikakken bayani.

Wuta da kuma wutar yola ta wasannin Olympics abin shaida ne na musamman ga mutane na kabilu da kasashe daban daban da ke iya harsuna daban daban da kuma bin addinai iri daban daban wajen neman samun matakin koli na wasannin motsa jiki da kuma zaman lafiya a duniya. A gun bikin kunna wutar da aka yi a wurin tarihi na Olympia na kasar Girka a ran 24 ga watan Maris, Jacques Rogge, shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya ya bayyana ma'anar mika wutar wasannin Olympics. Kuma ya ce,

"Cikin sahihanci ne, ina fatan kowa zai iya fahimtar ma'anar wutar wasannin Olympics. Ko da inda za a mika wutar, za ta kawo wa jama'a zumunci da zaman lafiya da kuma karfafa zukatansu wajen sa rai kan makoma. Dole ne a yi gasar wasannin Olympics da kuma mika wutar gasar cikin lumana. Wutar tana iya hada dukkan 'yan wasa da mutane na duniya tare, kuma tana iya hada dukkanmu wadanda ke ba da gaskiya ga ruhun Olympics."

Tare da aikin mika wutar gasar wasannin Olympics a duk duniya, ruhun Olympics ya samu yaduwa, kuma ra'ayoyin zaman lafiya da sada zumunci da kuma samun ci gaba su ma sun samu yaduwa. Birnin Dares Salaam na kasar Tanzania birni ne daya tak na Afirka wajen sa hannu a cikin aikin mika wutar. Charles Mattoke, mai kula da ayyukan wasannin motsa jiki na ma'aikatar sadarwa da al'adu da wasannin motsa jiki ta kasar Tanzania ya bayyana cewa,

"Wutar gasar wasannin Olympics ta alamanta zaman lafiya da hakuri da kuma kauna. Haka kuma ta ba mu wani labari, wato an ki yake-yake da yunkurin neman kawo baraka da hargitsi a duniya domin ta zama gidan dan Adam da ke da zaman lafiya da kauna."

1 2