Ra'ayi daban da Mr. Mustafa ya ambata a cikin jawabinsa shi ne a ran 20 ga watan Mayu na shekarar da muke ciki, gwamnatin kasar Iraki ta sanar da soke kwamitin wasannin Olymic na Iraki bisa dalilan "bai iya yin aiki kamar yadda ya kamata ba, da batun cin hanci", kuma ta kafa wani kwamitin rikon kwarya. Sakamakon haka, a ran 4 ga watan Yuni, kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya zargi gwamnatin Iraki da ta tsoma baki kan harkokin wasannin motsa jiki, kuma ya tsai da kudurin dakatar da matsayin kwamitin wasannin Olympic na Iraki a cikin kwamitin IOC. Sannan kuma, a ran 24 ga watan Yuli, an ki yarda da kungiyar 'yan wasan Iraki ta halarci gasar Olympic ta Beijing. Sabo da haka, gwamnatin kasar Iraki ta yi kokarin sulhuntawa, kuma ta amince da cewa za a kafa wani sabon kwamitin wasannin Olympic na Iraki ta hanyar yin zabe kafin karshen watan Nuwamba na shekarar da muke ciki. Daga karshe dai a ran 29 ga watan Yuli, kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa, wato IOC ya amince da kasar Iraki ta aika da wasu 'yan wasa da su halarci gasar Olympic ta Beijing.
Malama Dana Abdel Razak, wata 'yar wasan guje-guje na gajeren zango ta kasar Iraki, ita kadai ta samu izinin halartar gasar wasan guje-guje a gun gasar Olympic ta Beijing. A cikin watanni 2 da suka gabata, ta sha bakin ciki, kuma ta sha farin ciki. Lokacin da take magana da wakilanmu a filin saukar jiragen kasa na Beijing, ta maimaita magana "mafarki ya zama abin gaskiya" har sau da yawa. Ta ce, "Ina da wani mafarki, wato a gun bikin kaddamar da gasar Olympic, zan iya fitowa a madadin kasarmu. Yau, wannan mafarki ya zama abin gaskiya. Ina farin ciki, kuma ina jin alfahari sosai. Wannan ne karo na farko da na halarci gasar Olympic, gasar Olympic ta Beijing tana da kyau kwarai da gaske." (Sanusi Chen) 1 2
|