Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-05 18:42:27    
Kasar Iraki ta samu damar halartar gasar Olympic ta Beijing

cri

A 'yan kwanakin nan, ko kasar Iraki za ta iya halartar gasar Olympic ta Beijing ya zama wani batun da ke jawo hankulan jama'a. Bayan da kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya tsai da kudurin yarda da kungiyar wakilan 'yan wasan kasar Iraki ta halarci gasar Olympic ta Beijing, a lokacin karshe ne kasar Iraki ta sake komawa iyalan Olympic.

Da karfe 12 na ran 4 ga wata da tsakan dare, lokacin da wakilan kungiyar 'yan wasan Iraki sun fito a filin saukar jiragen sama na Beijing tare da furanni da kayansu, jama'ar da suka dade suna jiransu a can sun yi ihu sosai.

Kungiyar wakilan wasannin kasar Iraki tana kunshe da mutane 11, ciki har da 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle 2 da 'yan wasan tseren jirgin ruwa 2 da malam Tiras Odisho, shugaban kungiyar da shugaba Bashar Mustafa da babban sakatare Hussein al-Amidi na kwamitin wasannin Olympic na kasar Iraki. Membobin kungiyar suna farin ciki sosai. Malam Tiras Odisho ya ce, "Wannan gagarumin lokaci ne. Mun zo kasar Sin domin halartar gasar Olympic, kuma mun sake shiga iyalan Olympic. A wannan lokaci, mu da jama'ar kasarmu dukkanmu muna farin ciki sosai. Za mu daga tutar kasarmu a gun bikin kaddamar da gasar Olympic a madadin kasarmu. Wannan lokaci zai zama wani lokaci mai kyau sosai."

A waje daya kuma, malam Bashar Mustafa, shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasar Iraki ya ce, "Muna alfahari sosai domin za mu iya halartar gasar Olympic. Muna fatan kasar Iraki za ta zama wani muhimmin memba a cikin iyalan duk duniya. A karshe dai za mu iya halartar gasar Olympic, jama'ar Iraki su ne suka samu wannan nasara. Muna fatan 'yan wasan Iraki za su samu maki mai kyau. A da, muna da ra'ayi daban da gwamnatinmu, amma yanzu an riga an kau da shi. Mun samu nasarar aiwatar da shirinmu na halartar gasar Olympic ta Beijing."

1 2