Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-04 15:27:08    
Ingancin iska a Beijing ya kai matakin da ake bukata na yin wasannin Olympics

cri

Tun da aka shiga watan Auguta,an samu yanayi mai kyau cikin kwanaki uku a jere a nan birnin Beijing.ingancin iska ya kai matakin koli.A ran 3 ga watan Augusta a nan birnin Beijing wani jami'in ma'aikatar kiyaye muhalli na kasar Sin ya bayyana cewa an riga an kamala dukkan ayyukan da aka kayyade cikin matakan da aka dauka domin tabbatar da ingancin iska a nan birnin Beijing yayin da ake yin wasannin Olympics,ingancin iska a nan birnin Beijing ya kai matakin koli.Yayin da ake share fage ga wasannin Olympics,gwamnatin birnin Beijing da ma'aikatar kiyaye muhalli sun kama gaba sun kuma hada kansu da gwamnatoci na larduna 4 da birni Tianjin da ke kewayen birnin Beijing ciki har da lardi Hebei wajen yaki da gurbacewar iska duk domin tabbatar da ingancin iska yayin da ake yin wasannin Olympics. A gun taron menama labaran da aka shirya wannan rana,shugaban sashen kula da yaki da gurbacewar iska na ma'aikatar kiyaye muhalli na kasar Sin Mr Fan Yuansheng ya bayyana cewa an sami babbar nasara wajen yaki da gurbacewar iska cikin hadin gwiwa.ya ce "a watan Afril da watan July sashen sa ido na ma'aikatar kiyaye muhalli ya yi bincike kan yadda aka tabbatar da matakan tabbatar da ingancin iska. Gwamnatoci na wurare daban daban sun dauki tsauraran matakai wajen yaki da gurbacewar iska da wasu masana'ntu suka yi,da dakatar da masana'antun da suka gubata iska da kazanta muhalli da kuma motoci da tasoshin samara da mai,sun samu nasara, ta haka aka tabbatar da matakan da aka dauka domin tabbatar da ingancin iska.

Bisa sabon sakamakon da aka samu bayan da aka yi binciken yanayi, an ce daga watan Janairu zuwa watan Yuli na bana, an samu kwanaki 149 da aka samu iska mai inganci ko mafi nagarta a yankin birin Beijing,wato sun dau kashi 70 bisa dari.tun aka shiga watan Yuly, yawan carbon dioxide da carbon monoxide da ke cikin iska sun ragu da kashi 15 bisa dari da kuma kashi 27 bisa dari bisa ba na makamancin lokaci na shekarar bara.yawan kankannin abubuwan dake cikin iska da suka kazanta yanayi ya ragu da kashi 24 bisa dari. Ta haka ingancin iska ya karu a fili.

A lokacin da ake yin wasannin Olympics da wasannin nakasassu na Olympics,za a kuma dauki matakai da dama domin tabbatar da ingancin iska a yankin birnin Beijing,kamar su a rage yawan motocin da ke tafiye tafiye,da rubanya kokarin kula da wuraren gina gidaje da sauran ayyuka,haka kuma za a kara dakatar da masana'antun da suke gurbacewar muhalli, da rage hayakin da ake fitarwa da kuma sa ido kan muhalli.

1 2