Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-01 15:53:41    
Na babi na Rome--------"Mun shirya gasar wasannin Olympic cikin nasara"

cri

A ganinsa, dalilin da ya sa yanzu ana ganin cewa gasar wasannin Olympic ta Rome wata gasar wasannin Olympic da aka shirya cikin nasara, sabo da na daya, a lokacin da aka yi gasar wasannin Olympic ta Rome, an cimma nasarar watsa labaru kai tsaye, na dayan fa, shi ne gasar wasannin Olympic ta Rome ta hada da tsara fasalin wasannin Olympic da tsara fasalin birnin tare.

"A lokacin da aka yi gasar wasannin Olympic, talabiji ya riga ya shiga gidajen mutane, amma wannan shi ne karo na farko da aka watsa shirye-shiryen gasar wasanni ga dukkan duniya ta talabiji kai tsaye. Sabo da haka, wannan aiki yana da muhimmanci sosai, in akwai kuskure, sai dukkan duniya za su iya sani. Abin farin ciki ne mun cimma nasara, bugu da kari kuma, kafin gasar wasan Olympic da aka yi a Rome, dukkan gasannin wasan Olympic sun gina kauyukan gasar wasannin Olympic na tenti na tafi da gidammu, kuma kudaden da suka kashe wajen kafa wadanan kauyuka sun kai kimanin rabin kudaden da muka kashe a gasannin wasan Olympic, amma yayin da muka yanke shawarar gina dauwamammen kauyukan gasar wasannin Olympic, mun yi zato cewa, bayan da aka yi gasar wasannin Olympic, za a yi amfani da su, don su zama mazaunan ma'aikatan kasar. Ya zuwa yanzu, dukkan kauyukan gasar wasannin Olympic suna kasancewa yanzu.

A matsayinsa na firaministan gwamnatin kasar Italy har karo 7, Andreotti ya taba kai ziyara sau uku a kasar Sin, yayin da ya tabo maganar yadda ya dauki kasar Sin a zuciyarsa, ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu ba zai iya manta da halin da kasar Sin ke ciki ba.

Kasar Sin tana da kyaun gani sosai, haka kuma jama'ar Sin suna son baki sosai da ba a taba ganin irinsa ba, kuma sun shirya gasar wasannin Olympic da kyau. Ina fata in sake samun dama zuwa kasar Sin ziyara, ko da yake shekaruna ya kai 90 da haihuwa, ban iya doguwar tafiya ba. Amma na sani jama'ar Sin suna gudanar da ayyukansu cikin tsanake, ina fatan gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta sami nasara, muna fatan kasar Sin za ta yi gwaninta a dukkan fannoni.(Bako)


1 2