Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-01 15:53:41    
Na babi na Rome--------"Mun shirya gasar wasannin Olympic cikin nasara"

cri

A shekarar 1960, an cunna wutar gasar wasannin Olympic a birnin Rome. Domin waiwaye adon tafiya wajen shiryar gasar wasannin Olympic da aka yi a birnin Rome cikin nasara, wakilin gidan rediyon CRI ya gana da shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na Rome Giulio Andreotti, wanda ya taba zama firaministan gwamnatin Italy har sau 7.

A shekarar 1960, an shirya gasar wasannin Olympic a birnin Rome hedkwatar kasar Italy, 'yan wasannin da suka zo daga kasashe da yankuna 84, sun shiga cikin gasar wasannin Olympic da aka yi na wannan gami, 'yan wasannin da suka halarci gasar wasannin Olympic da aka yi a birnin Rome sun karya matsayin bajintar wasannin Olympic har sau 76, kuma sun karya matsayin bajintar duniya har sau 30. Kuma abin da ya kamata mu ambace shi, shi ne, a karkashin da kokarin da Italiyawa suka yi, rikicin siyasa na gaba da juna da aka bullo a gun gasar wasannin Olympic da aka yi a birnin Melbourne ya sami sasantawa, kuma sada zumunci da kokarin samun lambobin yabo sun zama babban taken wasannin Olympic, an daukaka gasar wasannin Olympic zuwa wani sabon matsayi. Shugaban kwamitin gasar wasannin Olympic na wancan lokaci Andreotti ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympic ta Rome ta nace bin hanyar cire siyasa da wasannin motsa jiki.

"Mun yi amfani da damar gasar wasannin Olympic don yin gyare-gyare ga wasu wuraren shakatawa, daga bisani kuma mun yi amfani da su don su zama dakuna da filayen gasar wasannin Olympic, wannan ba ma kawai ya bayyana wa dukkan duniya halin da Rome ke ciki ba, har ma ya yi tsimin kuddade wajen gina wasu sabbabin dakuna, sabo da haka, yawan kudaden da muka yi amfani wajen shirya gasar wasannin Olympic ba zai zarce yawan kudaden da muka yi kasafi ba, kuma an sami rarar kudade."


1 2