Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-31 15:09:38    
Hong Kong na kasar Sin

cri
 

Yanzu, a Hong Kong, an riga an aiwatar da manufar game da kasa daya mai tsarin mulki iri biyu daga duk fannoni, jama'ar Hong Kong suna tafiyar da harkokinsu su da kansu kwarai, suna ci gaba da bin tsarin mulki na jari hujja, suna zaman rayuwarsu ta hanyar da suka saba. Ya zuwa yanzu dai, Hong Kong tana kan matsayinta na cibiyar da ake yin harkokin ciniki da na kudade da zirga-zirga cikin 'yanci a duniya. Sabili da haka ana ganin cewa, yanzu, Hong Kong yanki ne da aka fi samun ci gaba a nahiyar Asiya da duk duniya. Sakamako da aka samu wajen aiwatar da manufar kasa daya mai tsarin mulki iri biyu yana gwada misali mai kyau ga daidaita matsalar Taiwan ta kasar Sin.

Hong Kong da aka komo da ita a karkashin mulkin kasar Sin tana jawo hankulan kasa da kasa sosai. Bisa izni da ta samu daga wajen gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, Hong Kong ta riga ta kulla yarjejeniyoyi guda 63 a tsakaninta da kasashe da yankuna dabam daban na duniya. Ya zuwa ran 31 ga watan Mayu na shekarar 2002, yawan kasashe da yankuna wadanda suka bai wa mutane masu rike da fasfo din Hong Kong izinin su shiga cikinsu ba tare da biza ba ya kai 112. Duk wadannan sun ba da shaida sosai cewa, gamayyar kasa da kasa ta amince da manufar da ake bi a Hong Kong game da kasa daya mai tsarin mulki biyu.


1 2