A ran 1 ga watan Yuli na shekarar 1997, aka kawo karshen mulkin mallaka da kasar Britaniya ta shafe shekaru 150 tana yi a Hong Kong, wato ke nan aka komo da Hong Kong a karkashin mulkin kasar Sin. Kuma daga wannan rana ne, Hong Kong ta shiga cikin wani sabon lokaci da aka fara aiwatar da manufar kasar Sin daya mai tsarin mulki iri biyu, jama'ar Hong Kong sun sami ikon tafiyar da harkokinsu su da kansu.
A ran 1 ga watan Yuli na shekarar 2002, tsohon shugaban kasar Sin Jiang Zemin ya halarci taro da aka shirya a Hong Kong don murnar ranar cika shekaru 5 da komo da Hong Kong a karkashin mulkin kasar Sin. A cikin jawabin da ya yi a gun wannan taron, Mr. Jiang Zemin ya bayyana cewa, shekarun nan 5 shekaru ne da aka sami nasara wajen aiwatar da manufar kasa daya mai tsarin mulki iri biyu, kuma shekaru 5 ne da gwamnatin yankin musamman na Hong Kong wadda ke karkashin shugabancin Malam Dong Jianhua ta hada kanta da mutanen bangarori dabam daban na Hong Kong domin su yi ta samun ci gaba wajen kawar da wahalhalu. Bayan haka ya nuna cewa, komo da Hong Kong a karkashin mulkin kasar Sin ke da wuya, sai aka gamu da rikicin darajar kudade mai tsanani da ya faru a nahiyar Ashiya, da kuma munanan sauye-sauyen guraben tattalin arzikin duniya. Amma bisa goyon bayan gwamnatin tsakiya na kasar Sin, kuma a karkashin shugabancin gwamnatin Hong Kong, mutanen bangarori dabam daban na Hong Kong sun hada guiwarsu, suka yi kokari sosai, suka daidaita matsaloli da dama na zamantakewar al'umma da tattalin arziki, suka tabbatar da zaman mai karko a Hong Kong.
1 2
|