Hadaddiyar kunagiyar 'yan fasahar jama'ar jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta inda Mr. Tseten Dorje ke aiki ta sauke nauyin musamman domin tattara da shirya da kuma kiyaye da yin binciken al'adu da fasahar jama'a na jihar Tibet, hadaddiyar kungiyar tana hade da mutane masu sana'a da yawa da wadanda ba na lokacin aiki ba wadanda kuma suke dukufa kan aikin kiyaye al'adun jama'a na jihar. Mr. Tseten Dorje ya ce,
"Yanzu hadaddiyar kungiyarmu tana da mambobi fiye da 200, wadanda suke yin wallafe-wallafe a kowace shekara, daga cikin littattafan da suka rubuta, da akwai na harshen kabilar Tibet da na kabilar Han, wasu mambobin kunagiyar suna dukufa kan aikin binciken adabin jama'a, wasun kuma suna yin binciken al'adun fasaha na zamani ko kuma na gargajiya. Ban da wannan kuma da akwai wasu mambobi wadanda suke aikin rubuta littattafai kan wani fanni kawai, wato kamar fannin turaren wuta na kabilar Tibet, ko fannin kayayyakin fadi ka mutu, ko kuma fannin tufafi, ana iya samun littattafai da yawa da aka rubuta kan wadannan fannoni." 1 2 3
|