Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-28 15:15:50    
Bayani kan halin da ake ciki a jihar Tibet wajen bunkasa al'adun jama'a

cri

A farkon shekaru 90 na karnin da ya wuce, kuma bisa tallafi da taimakon da hukumomin da abin ya shafa na gwamnatin kasar Sin suka bayar, sassan al'adu da madaba'u na jihar Tibet sun shafe shekaru 14 suna aikin shiryawa manyan littattafai 3 na al'adun jama'a na jihar, wadanda ke kunshe da kalmomi miliyan 3 da dubu 840 na harshen Tibet. Mr. Tseten Dorje, shugaban hadaddiyar kunagiyar 'yan fasaha ta jama'ar jihar Tibet ya bayyana cewa,

"Ba a taba buga wadannan manyan littattafai 3 a tarihin jihar Tibet ba, gwamnatin kasar Sin ta ware makudan kudade domin wannan aiki, na yi lissafi cewa jimlar kudin da aka ware ta kai kudi Sin wato daga Yuan miliyan daya zuwa miliyan 2".

Mr. Tseten Dorje ya kuma bayyana cewa, ba mai yiwuwa ba ne a kammala irin babban aikin al'adu mai girma kamar haka a tsohon zamani a jihar Tibet.

Daga karshen shekaru na 50 na karnin da ya wuce, kuma a karkashin kulawar hukumomin gwamnatin kasar Sin, an mai da al'adun jama'a na jihar Tibet a matsayin adabi da fasaha, matsayin 'yan fasahar jama'a shi ma ya fara daguwa. Mr. Tsetan Dorje ya ce,

"Matsayin 'yan fasaha na jama'a ya dagu, sun sami 'yanci sosai, wasunsu sun ci zaben zama mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, mu 'yan fasahar binciken kayayyakin duwatsu masu daraja da lu'ulu'u mu ma mun samu mukami, an dauke mu tamkar abu mai daraja na kasar Sin, mun samu sharuda masu kyau wajen albashi da sauran fannoni, lalle an yi manyan sauye-sauye."


1 2 3