Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-25 20:12:00    
Tawagar 'yan wasannin Olympics ta kasar Sin ta kafu a hukunce

cri

Bisa labarin da muka samu, an ce, wannan ita ce wata tawagar 'yan wasannin Olympics ta kasar Sin da aka fi samun yawan mutane da shigar yawan gasanni a tarihi. Amma Cui Daling, wani mataimakin shugaba daban na tawagar ya nuna cewa, dalilin da ya sa aka iya samun 'yan wasa masu dimbin yawa kamar haka shi ne sabo da kasar Sin mai masaukin gasar ne, ya kamata tawagar kasar Sin ta fahimci kwarewarsu kamar yadda ya kamata. Kuma ya kara da cewa,

"Sabo da mu ne mai masaukin gasar wasannin Olympics, shi ya sa mun samu iznin shiga wasu gasanni na kwallaye tsakanin kungiya-kungiya da kuma gasannin tsakanin mutum dai dai kai tsaye bisa ka'idojin hadaddun kungiyoyin gasanni tsakanin mutum dai dai na duniya, sabo da haka mun samu wannan babbar tawaga. Ko da yake yawan 'yan tawagar ya yi yawa, amma ita ba tawaga mafi karfi ba ce, watakila abokan karawarmu sun fi kwarewa."

Bisa shirin gasanni da aka tsara, watakila kungiyar 'yan wasan harbe-harbe ta kasar Sin za ta samu lambar zinariya ta farko a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing, maganar babban malamin koyar da wasan Wang Yifu ta bayyana burin dimbin 'yan wasa na kasar Sin. Ya ce,

"Yau, tawagar kasar Sin ta kafu. Ba za mu kauce wa burin mutane ba, kuma tabbas ne za mu yi iyakacin kokarinmu a gun gasar."

Ban da wannan kuma Liu Peng, shugaban tawagar ya bayyana cewa, sashen wasanni na kasar Sin ya riga ya yi shiri sosai don gasar wasannin Olympics ta Beijing. Tabbas ne zai yi namijin kokari domin samun maki mai kyau. A waje daya kuma, sashen zai kara yin cudanyar aminci tare da sassan wasanni na kasashen waje don kara zumuncinsu da kuma sa kaimi ga bunkasuwar sha'anin Olympics.(Kande Gao)


1 2