A ran 25 ga wata, wato lokacin da ya rage sauran makwanni biyu da bude gasar wasannin Olympics ta Beijing, tawagar 'yan wasa ta kasar Sin da za ta shiga gasar ta kafu a birnin Beijing. Ana iya samun 'yan wasa na tawagar kasar Sin 639, shi ya sa tawagar ta zama wata tawaga ce da aka fi samun yawan 'yan wasa da yawa a tarihi. Haka kuma yawan gasanni da tawagar kasar Sin za ta sa hannu a ciki ya zo na farko a cikin dukkan tawagogin da za su shiga gasar. Shugaban tawagar 'yan wasannin Olympics ta kasar Sin kuma shugaban babbar hukumar wasanni ta kasar Sin Liu Peng ya bayyana cewa, a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing, tawagar kasar Sin za ta yi namijin kokari domin samun maki mai kyau, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar sha'anin Olympics. To yanzu ga cikakken bayani.
A gun taron kafuwar tawagar 'yan wasannin Olympics ta kasar Sin, Duan Shijie, mataimakin shugaban tawagar ya bayyana cewa, game da yawancin 'yan tawagar, wannan shi ne karo na farko na shiga gasar. Kuma ya kara da cewa,
"Tawagar 'yan wasannin Olympics ta kasar Sin tana kunshe da mutane 1099, wadanda za su shiga manyan gasanni 28 da kuma kananan gasanni 38 na gasar wasannin Olympics ta Beijing. Haka kuma a cikin tawagar, akwai 'yan wasa 639, a ciki, 'yar wasan tsinduma cikin ruwa daga kan dandamali Guo Jingjing, da dan wasan harbe-harbe Tan Zongliang, da kuma dan wasan kwallon kwando Li Nan sun riga sun shiga wasannin Olympics har sau uku, game da sauran 'yan wasa 469 wannan shi ne karo na farko wajen shiga gasar."
1 2
|