Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-23 17:26:26    
Ziyara zuwa cibiyar 'yan jarida ta wasannin Olympic na Beijing

cri

Ita ma wannan cibiya an samar da kayan aiki ga 'yan jarida, kamar su internet, inda 'yan jarida za su iya amfani da internet ta hanyar yin amfani da kati, inda akwai tebura kimanin dari tara da tamanin da aka samar da wannan hidima ta internet. Akwai kuma wuraren cin abinci, da wuraren shaye shaye domin hutawa da kuma hidimar banki na ATM, da wuraren tausa da na motsa jiki da manyan dakunan taro.

Babbar cibiyar ta 'yan jarida mai hawa ukku tana da fadin murabba'in mita dubu sittin, kuma itace cibiyar 'yan jarida mafi girma a tarihin wasannin Olympics na duniya.

Da misalain karfe hudu da rabi ne muka kammala ziyara a wannan babbar cibiya 'yan jarida (MPC), kuma muka kamo hanyar komowa CRI, mun iso CRI da nisalin karfe biyar na yamma. (Lawal)


1 2