Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-23 17:26:26    
Ziyara zuwa cibiyar 'yan jarida ta wasannin Olympic na Beijing

cri

Da misalin karfe daya da rabi na ranar 22 ga watan Yuli ne tawagar ma'aikatan gidan rediyon CRI, akasarinsu baki, ta tashi zuwa cibiyar 'yan jarida ta wasannin Olympic ta Beijing, wadda aka kaddamar a ranar takwas ga wannnan wata na Yuli.

Mun isa wannan cibiyar 'yan jaridu da misalign karfe biyu na rana, inda ba tare da bata lokaci ba jami'an tsaro suka tantance mu domin samun damar shiga wannan katafaren gini na cibiyar 'yan jaridu. Mun fara wannan ziyara ne a babban ginin daya kunshi cibiyoyin 'yan jarida biyu, wato Cibiyar yada labaru ta kasa da kasa wato (IBC) da kuma Cibiyar 'yan jarida ta kasa da kasa ta Beijing, wato (BIMC). Mun fara wannan ziyara a cibiyar 'yan jarida ta kasa da kasa ta Beijing (BIMC) a karkashin jagorancin wani jami'I mai bayar da jagoranci tare. An nuna mana kayan aiki na 'yan jarida na zamani wato irin na digital domin amfanin 'yan jarida daga ko ina cikin duniya. Wannan cibiya ta BIMC zata iya bayar da hidima ga 'yan jarida kimanin dubu goma, sannan kuma a kowace rana za ta rinka shirya taron manema labaru , inda za'a rinka gayyato jami'an gwamnati domin amsa tambayoyin manema labaru kan irin ci gaban da China ta samu a fannin tatalin arziki, kyautata yanayin mahalli da abinci da kuma yanayin tsaro.

Bayan mun kammala zagayawa a cibiyar 'yan jarida ta kasa da kasa ta Beijing (BIMC) sai kuma muka wuce zuwa cibiyar yada labaru ta kasa da kasa (IBC) wadda ta kasance a matsayin tushe na watsa shirye shiryen wasannanin Olympics , kuma hedkwatar 'yan jarida masu daukar rahoto su kimanin dubu goma sha shidda da za su zo daga kasashe kimanin dari da ashirin. Girman wannan gini na IBC zai kai murabba'in mita dubu takwas da dari hudu, Akwai dakunan watsa shirye shirye da aka gina a wannan cibiya, wannan kuma ko wane dakin watsa shirye shirye abn samar da kayan aiki na zamani. Daga cikin wadannan dakuna akwai na gidan rediyon CRI, wanda zai rinka watsa shirye shiryensa kai tsaye a kan wasannin Olympics zuwa ga kasashen duniya.

Bayan mun kammala ganewa idonmu abubuwan dake cikin wadannan cibiyo biyu wato BIMC da IBC wadanda dukkansu suna a cikin gini daya, sai kuma muka fita zuwa babban cibiyar 'yan jarida wadda take gefe daya. Ita ma dai sai da jami'an tsaro suka tantance mu, sannan kuma aka ba mu katin izinin shiga wanda muka rataya a wuya. Babbar cibiyar 'yan jarida ta kasance a matsayin babbar tashar da 'yan jarida na kasashen duniya kimanin dubu bakwai za su yi aiki a ciki, domin yada labaru game da wasannin Olympics. Daga cikin 'yan jaridar akwai na talbijin, da na rediyo da kuma na jaridu.

An kiyasta cewa yayin gasar wasannin na Olympics za'a gudanar a tarukan 'yan jarida kimanin dari biyar a wannan babbar cibiyar 'yan jarida. Sannan kuma za'a yi amfani da wannan cibiya a wasannin Olympics na nakasassu.

1 2