
Ya zuwa yanzu, ana kiyaye dakin Tingilguan bisa salon gine-gine na gargajiya. Dukkan sabis suna sanya tufafi irin na gargajiya da aka taba sanyawa a fada. Mutanen da suka ci abinci a dakin Tingliguan su kan gane cewa, suna cin abinci a cikin dakin cin abinci na sarakuna. Sa'an nan kuma, ko wane abinci da ake samarwa a dakin Tingliguan yana da labarinsa, shi ya sa a lokacin cin abinci, sabis su kan yi wa mutane bayani kan wadannan labaru. Zhao Tongyi ya yi shekaru 30 ko fiye yana aiki a dakin Tingliguan, ya gaya mana cewa, 'Dakin Tingliguan wani gine ne da aka gina bisa salon gine-gine na zamanin daular Qing na kasar Sin, kuma an yi masa ado a ciki bisa yadda salon fadar sarakuna. Mutane su kan ga bambanci in suka isa wurin. Akwai labaru da dama game da abincin da muke samarwa a nan. Mutane suna iya cin abinci da kuma kara fahimtarsu kan al'adun abinci.'
Domin maraba da gasar wasannin Olympic ta Beijing, an yi kwaskwarima kan wurin yawon shakatawa na Yiheyuan, kazalika kuma, an ba da hidimomi daga dukkan fannoni a nan domin biyan bukatun baki daga kasashen waje. 1 2
|