Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-22 19:08:27    
Fadar shakatawa na sarakuna a yanayin zafi wato Summer Palace mai suna Yiheyuan a Beijing

cri

Kasar Sin ta yi suna ne saboda fasahar zayyana lambuna. Fadar shakatawa ta sarakuna a yanayin zafi wato Summer Palace da muke kiranta Yiheyuan da ke arewa maso yammacin Beijing, lambun sarakuna ne da aka yi mata cikakken adana a kasar Sin. Yana kasancewa wani dakin ajiye kayayyakin tarihi, kuma an gina shi ne bisa fitacciyar fasahar gine-gine da al'adu da kuma fasaha. Ba kawai fadar yanayin zafi ta shahara a gida ba, har matafiya masu yawa daga kasashen waje sun mayar da shi daya daga cikin wuraren da tilas ne su kai musu ziyara. Yau ma bari mu yi yawo a cikin wannan lambun sarakuna da aka fara ginawa a zamanin daular Qing ta kasar Sin, wato yau da shekaru 250 ko fiye da suka wuce.

A ran 2 ga watan Disamba na shekarar 1998, hukumar ilmi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta nada wurin yawon shakatawa na Yiheyuan a matsayin wurin tarihi na al'adu na duniya. A ko wace shekara, mutane suna ta kawo wa fadar yanayin zafi ziyara daga gida da kuma waje. Madam Li Kun, wata jami'ar hukumar kula da wurin yawon shakatawa na Yiheyuan ta yi mana karin bayani cewa,'A matsayinsa na abun ishara a tarihin lambuna na kasar Sin da kuma dukiyar al'adu ta duniya, fadar yanayin zafi ta kan karbi masu yawon shakatawa har da miliyan 1 a ko wace shekara, ciki yawan wadanda suka zo daga kasashen waje ya wuce kashi 15 cikin dari. Fadar yanayin zafi ta nuna muhimmanci sosai wajen nuna kyakkyawar surar Beijing da kuma yin mu'amala tare da kasashen waje.'

Akwai ni'imtattun wurare da yawa a cikin fadar, sa'an nan kuma, wannan wurin yawon shakatawa yana matsayin dakin ajiye kayayyakin tarihi da na al'adu. A shekarun baya, an yi kwaskwarima kan muhimman ni'imtattun wurare a matakai daban daban a fadar, ta haka wannan wurin yawon shakatawa mai dogon tarihi ya sake nuna kyan ganinsa. Madam Li ta gaya mana cewa,'A matsayinsa na wurin tarihi na al'adu na duniya, a ko wace shekara hukumarmu da gwamnatin kasar Sin sun zuba makudan kudade tare da aikawa da kwararru da yawa kan kiyaye wurin yawon shakatawa na Yiheyuan, domin tabbatar da ganin zai sami ci gaba mai dorewa, haka kuma, zai nuna kyan ganinsa a matsayin lambun sarakuna kamar yadda yake zama a farkon kafuwarsa wato yau da shekaru 250 ko fiye da suka wuce.'

An yada fasahar zayyana lambuna ta kasar Sin sosai a wurin yawon shakatawa na Yiheyuan, akwai ni'imtattun wurare masu ban mamaki da yawa a nan.

Wata doguwar rumfa tana kasancewa kudancin babban dutsen Wanshoushan a cikin fadar, tana fuskanta tabkin Kunminghu, tsawonta ya kai mita 728, ita ce doguwar rumfa ta gargajiya mafi tsayi a duniya. Mambobin sarakuna sun gina ta ne domin more idonsu da ni'imtattun wurare na fadar a yayin da ake ruwan sama ko kuma dusar kankara. A ko wane ginshikin rumfar an yi zane-zane, yawan zane-zanen ya wuce dubu 8, kuma suna shafar ni'imtattum wurare da furanni da tsuntsaye da kifaye da tsutsotsi da labaru game da mutane. Wannan rumfa tana daya daga cikin ni'imtattun wuraren da masu yawon shakatawa suka fi son ziyara, inda suke iya kallon ni'imtattun wurare, haka kuma, sun iya kara saninsu kan al'adun kasar Sin mai dogon tarihi bisa wadannan kyawawan zane-zane. Ewa, wata mutumiyar kasar Poland ta kawo wa kasar Sin ziyara sau da dama. A ko wane karon da ta yi bulaguro a wurin yawon shakatawa na Yiheyuan, ta kan nuna babban yabo ga wannan rumfa. Ta ce,'Wannan rumfa na da kyan gani sosai. Ban taba ganin irin wannan rumfa mai kyan gani kamar haka a sauran wurare na duniya ba, musamman ma bayan da aka yi mata kwaskwarima, ta kara kyan gani.'

Baya ga ni'mtattun wurare da wuraren tarihi masu tarin yawa, a cikin wurin yawon shakatawa na Yiheyuan, akwai wani wuri da ya cancanci cin abinci irin na sarakuna, sunansa shi ne Tingliguan. A can da, sarakuna da matansu su kan saurari wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin da kuma gudanar da sauran harkokin nishadi a nan, amma bayan kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, dakin Tingliguan ya zama wurin da aka karbi baki masu girma daga kasashen waje.

1 2