Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-22 14:41:58    
Yaya matsayin farin ciki yake ga al'ummomin Zimbabuwe

cri

A karshen shekarun 1980, Zimbabuwe ta taba zama kasar da ta fi inganta wajen manyan ayyuka a kudancin Afirka, kuma 'yan kasar ma sun taba zaman rayuwa cikin wadata. Amma irin wannan hali bai dade ba. A shekarar 1999, jam'iyyar neman sauyin dimokuradiyya, wadda ta kasance jam'iyyar adawa mafi girma a kasar, ta kafu bisa goyon bayan kasashen yammaci. Don fuskantar jam'iyyar da kuma gyaran mallakar kashi 70% na gonakin kasar da fararen fata da ba su kai 1% na mutanen kasar suka yi, jam'iyyar ZANU-PF ta gabatar da manufar gyaran filayen kasar. A shekarar 2000. Gwamnatin Zimabuwe ta kwace wa fararen fata dimbin gonaki, sabo da haka, shugaba Mugabe ya bata da kasashen yammaci cikin sauri.

Daga baya, ko da yake shugaba Mugabe ya sake cin zaben shugaban kasar har sau biyu, wato a watan Maris na shekarar 2002 da kuma watan Yuni a shekarar da muke ciki, amma kasashen Birtaniya da Amurka da kuma 'yan hamayyarsa ba su ko daina zarginsa da tafka magudi ba, sa'an nan, kasashen yammaci na kara kakaba wa Zimabuwe takunkumi mai tsanani.

Masu sauraro, mene ne farin ciki? Watakila akwai amsoshi sama da dubu ga tambayar. Amma a ganin jama'ar Zimbabuwe, yanzu farin ciki a gare su shi ne a kawo karshen matsalar siyasa tun da wuri, kuma a farfado da tattalin arziki cikin sauri. Watakila bisa yarjejeniya da gwamnatin ta cimmawa tare da jam'iyyar adawa, jama'ar Zimbabuwe sun riga sun kusanci farin ciki sosai.(Lubabatu)


1 2