Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-22 14:41:58    
Yaya matsayin farin ciki yake ga al'ummomin Zimbabuwe

cri

Jiya 21 ga wata, watakila za ta kasance ranar da jama'ar Zimbabuwe, wadanda suka sha fama da tashe-tashen hankulan siyasa, za su tuna da ita a nan gaba. Sabo da a ran nan, shugaban kasar Zimbabuwe, Robert Gabriel Mugabe ya cimma yarjejeniya tare da shugaban jam'iyyar adawa, Morgan Tsvangirai, inda suka yi alkawarin kawo karshen matsalar siyasa ta kasar tun da wuri ta hanyar yin shawarwari tsakanin jam'iyyunsu. A ran nan, babban sakataren MDD, Ban Ki-moon ya bayar da sanarwa, inda ya nuna maraba ga daddale yarjejeniyar da bangarorin biyu suka yi.

A farkon watan nan da muke ciki, jami'ar Michigan ta kasar Amurka ta kaddamar da wani rahoton bincike a kan kashi 90% na mutanen duniya dangane da matsayin farin cikinsu. Daga cikin kasashe 97 da aka yi wannan bincike, Zimbabuwe ce ta zo ta karshe, wato kashi 4% na jama'ar kasar ne kawai suna "farin ciki". Ba shakka, rahoton na da wani abin son zuciya a ciki, amma duk da haka, a cikin 'yan shekarun baya, sakamakon tashe-tashen hankula a Zimbabuwe da kuma takunkumi mai tsanani da kasashen yammaci suka kakaba mata, gaskiya ne yawancin jama'ar Zimbabuwe suna cikin mawuyacin hali. Kasancewar Zimbabuwe a kudu maso gabashin Afirka, tana daga cikin kasashe masu matsakaicin girma ko a wajen fadinta ko kuma a fannin yawan al'umma. Amma duk da haka, kasar ta zo farko a wasu fannonin rashin jin dadi.

Zimababuwe ta zo farko a wajen samun hauhawar farashin kayayyaki. Bisa adadin da gwamnatin Zimababuwe ta bayar da dumi-duminsa, an ce, a halin yanzu, yawan hauhawar farashin kayayyaki ya kai har kashi 2,200,000% a kasar, wanda ya zo na farko a duniya. Amma a ganin masanan ilmin tattalin arziki masu zaman kansu, hauhawar farashi na hakika ya iya wuce adadin.

Sa'an nan, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, takardun kudin da babban bankin Zimbabuwe ya kaddamar sun fi daraja a duniya, musamman ma takardar kudi mai daraja miliyan 500 da kasar ta kaddamar a ran 15 ga watan Mayu na wannan shekara.

Bayan haka, jama'ar Zimbabuwe sun fi karancin tsawon rayuwa a duniya. A halin yanzu dai, matsakaicin tsawon rayuwar jama'ar Zimbabuwe ya kai 37 ne kawai. Yawan mutuwar jarirai da kuma yawan kamuwa da cutar Sida, wanda ya wuce har kashi 1/5 na mutanen kasar, dukansu suna cin ran kasar. Bayan haka, matsalar karancin abinci ita ma tana barazana ga jama'ar Zimabuwe.

1 2