Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-21 18:48:43    
Beijing tana daukar matakai domin rage iskar da motoci suke fitarwa

cri

Shehu malami Liu Xian ya dade yana nazarin motoci a cibiyar nazarin motoci ta Beijing yana ganin cewa, rage iskar da motoci ke fitarwa wani aiki ne da ke bukatar dogon lokacin gudanarwa. Ya kuma ba da shawara kan kayyade motocin da suka gurbata muhalli sosai bayan gasar wasannin Olympic. Ya ce,'Dole ne a kara yi wa wadannan motoci bincike a ko wace shekara, a kara kudin bincike bisa tsawon shekarun da ake amfani da su, ko kuma direbobi su biya kudin gurbata muhalli bisa iskar da motocinsu ke fitarwa, ta haka kudin da aka biya domin yin amfani da wadannan motoci zai karu, direbobin za su yi watsi da motocinsu kafin wa'adin aikinsu ya cika.'

 

Baya ga wadannan matakai, Beijing ta dauki matakan wucin gadi na kayyade zirga-zirga a lokacin gasar wasannin Olympic. Kayyade zirga-zirgar motoci bisa lambobinsu ya fi jawo hankali. A ko wace rana motoci fiye da miliyan 1 sun daina gudu a kan titunan Beijing a sakamakon wannan mataki, ta haka an rage iskar da motoci ke fitarwa sosai. Zheng Jie, wata mazauna Beijing ta bayyana cewa,'Wannan mataki lamari ne mai kyau ga Beijing. Ya kyautata zirga-zirgar Beijing, ya kuma kyautata iskar Beijing. Za a bude gasar wasannin Olympic ba da dadewa ba. Wannan mataki zai kara kyautata iskar Beijing a lokacin gasar wasannin Olympic.'

A sakamakon wannan mataki, mutane har sau fiye da miliyan 4 suna amfani da motocin al'umma a ko wace rana. Shi ya sa Beijing ta dauki sauran matakai domin yin iyakacin kokarin rage illar da kyayyade zirga-zirgar motoci ke kawo wa mazauna Beijing a ayyukansu da zaman rayuwarsu.(Tasallah)


1 2