Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-21 18:48:43    
Beijing tana daukar matakai domin rage iskar da motoci suke fitarwa

cri

Domin cika alkawarin shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing ba tare da gurbata muhalli ba, a shekarun baya, hukumar Beijing ta yi kokari sosai wajen rage iskar da motoci suke fitarwa, ta kuma sami kyakkyawan sakamako a wannan fanni. Saboda kusantowar gasar wasannin Olympic, Beijing ta dauki sauran matakan kayyade zirga-zirga domin tabbatar da zirga-zirga yadda ya kamata da kuma ingancin iska mai kyau a lokacin gasar wasannin Olympics.

Tun bayan da Beijing ta sami nasarar samun bakuncin shirya gasar wasannin Olympic a shekarar 2001 har zuwa yanzu, ingancin iska na Beijing yana ta jawo hankulan kasashen duniya sosai. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan iskar da motoci ke fitarwa ya kai sulusin abubuwa masu gurbata iska a Beijing. Saboda haka, Beijing ta dauki matakai da dama domin sassauta wannan matsala. 

A cikin shekaru 5 da suka wuce, Beijing ta kara zuba makudan kudade kan raya babban zirga-zirga na jama'a da kebe hanyoyin musamman domin kayan ababen hawa. Ta kuma mayar da raya babban zirga-zirga na jama'a a gaba da kome.

Ban da wannan kuma, Beijing ta yi amfani da kudade masu tarin yawa wajen yin watsi da tsoffin kayan ababen hawa da taksi da sayen sabbabi. Tun daga shekarar 2005, Beijing ta sayi kayan ababen hawa dubu 14 da ke amfani da makamashi maras gurbata muhalli. Ya zuwa yanzu yawan kayan ababen hawa da ke amfani da makamashi maras gurbata muhalli ya kai kashi 92 cikin dari bisa jimlar kayan ababen hawa kusan dubu 20 da ke gudu a Beijing. Beijing ta riga ta zama birni mafi yawan motocin al'umma da ke amfani da makamashi maras gurbata muhalli.

Feng Xingfu, mataimakin darektan kamfanin kula da babban zirga-zirga na jama'a na Beijing ya yi karin bayani da cewa,'A cikin shekaru 3 da rabi da suka wuce, mun yi amfani da kudin Sin yuan biliyan 13 domin yin watsi da tsoffin motocin al'umma dubu 11 da 162, da sayen sabbabi dubu 12 da 509 da ke amfani da makamashi maras gurbata muhalli. Ma iya cewa, manyan motocin kamfaninmu na kashi 97 cikin dari ko fiye suna iya tabbatar da ma'aunin da aka tsara kan iskar da motoci ke fitarwa.'

Ban da wannan kuma, a farkon wannan shekara, Beijing ta dauki jagoranci wajen aiwatar da ma'auni mafi tsaurara kan iskar da motoci ke fitarwa a kasar Sin. Sa'an nan kuma, Beijing ta hana motocin da suke gurbata muhalli sosai su yi zirga-zirga a kan hanya a lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing, wadanda yawansu ya kai kashi 10 cikin dari bisa jimlar motoci a Beijing.

1 2