Manazarta masu aikin likitanci na jami'ar Pennsylvania ta kasar Amurka sun buga wani rahoto a kan wata mujallar likitanci, cewa bayan da suka gudanar da bincike kan tsoffin mata masu shan taba, sun gano cewa, yiyuwar kamuwa da ciwon sankarar huhu ga masu shan taba da su kan motsa jiki ta ragu da kashi 35 cikin dari idan an kwatanta da wadanda ba su son motsa jiki. Amma Catherine Schmitz, mai kula da binciken ta jaddada cewa, ta sakamakon binciken da suka gudanar, kada a dauka cewa, wato idan aka kara motsa jiki, to za a iya shan taba ba tare da damuwa ba. Idan masu shan taba suna son rage hadarin kamuwa da ciwon sankarar huhu, muhimmin abu shi ne tsai da kudurin yin watsi da shan taba.
Manazarta sun yi amfani da kididdigar da aka samu ta binciken da aka gudanar kan lafiyar jikin mata a jihar Lowa ta kasar Amurka. Tun shekara ta 1986, aka fara gudanar da binciken ga tsoffin mata, kuma ya zuwa karshen shekara ta 2002, an samu labarun mata da yawansu ya zarce dubu 36, kuma 777 daga cikinsu sun kamu da ciwon sankarar huhu. Kuma an yi hasashen cewa, 125 daga cikin wadanda suka kamu da ciwon ba su shan taba ko kadan yayin da 177 daga cikinsu sun taba yin watsi da shan taba cikin nasara, ban da wannan kuma 475 daga cikinsu su kan shan taba har kullum. Haka kuma nazarin yana ganin cewa, wadanda suka fi saukin kamuwa da ciwon sankarar huhu su ne mutane masu shan taba kuma ba su son motsa jiki.
1 2 3
|