Nazarin kimiyya ya bayyana cewa, taba za ta iya haifar da munanan illoli iri fiye da 4000 idan aka kuuna ta, kuma wadanda su kan sha taba suna iya kamuwa da cutar sankara da ta zuciya da hauhawar jini da dai sauransu. A ko wace shekara, mutane kusan miliyan biyar ne suke mutuwa sakamakon cututtukan da ke da nasaba da shan taba. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku wani bayani kan cewa, kara motsa jiki ga masu shan taba zai iya rage hadarin kamuwa da ciwon sankarar huhu.
Kowa ya sani, shan taba yana yin mumunar illa ga lafiyar jikin dan Adam, amma duk da haka, mutane masu dimbin yawa su kan shan taba. Ta wani sabon binciken da suka gudanar, kwararru masu aikin likitanci na kasar Amurka sun ba da shawarar cewa, ya kamata mutanen da ba su son yin watsi da shan taba da kuma wadanda ba su iya yin watsi da shan taba su kara motsa jiki, ta haka za su iya rage hadarin kamuwa da ciwon sankarar huhu.
1 2 3
|