Shekarar da muke ciki shekara ce da aka kimanta da kuma tattauna wannan burin samun bunkasuwa na matsakaicin lokaci, amma ana nuna damuwa sosai ga halin da Afirka ke ciki wajen cimma burin.
A cikin sanarwar da kungiyar G8 ta bayar a ran 8 ga wata, ta amince da cewa, kasashen Afirka suna tinkarar kalubale mai tsanani wajen cimma burin samun bunkasuwa. Haka kuma babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya yi bayani a gun taron manema labarai da aka shirya a ran 7 ga wata, cewa kasashen Afirka sun riga sun kauce hanya wajen cimma burin. Ba a bukaci kungiyar G8 da ta samar da sabon jari ba, muddin ta cika alkawarin da ta yi wajen samar da taimako ga kasashen Afirka, to za a iya tabbatar da samun isassun kudaden da Afirka ke bukata wajen cimma burin samun bunkasuwa da aka tsara a shekara ta 2000.(Kande Gao) 1 2
|