Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-09 16:15:17    
G8 ta daina yin kokarin a zo a gani kan batun Afirka ko da yake ta yi alkawari sosai

cri

A 'yan shekarun nan da suka gabata, har kullum a kan dora muhimmanci sosai kan batun Afirka a gun taron koli na kungiyar kasashe 8 masu aizikin masana'antu a duniya wato G8. Kuma a gun taron koli na kungiyar G8 na shekarar da muke ciki da ake yi a tafkin Toyako na kasar Japan, batun Afirka ya sake zama daya daga cikin muhimman batutuwan da ake tattaunawa a kai. Ajanda ta farko ta taron koli na bana ita ce taron tattaunawa tsakanin kungiyar G8 da kasashe 7 na Afirka. Haka kuma a gun taron aiki na kungiyar da aka shafe yini daya ana yinsa a ran 8 ga wata, an sake mai da hankali wajen tattaunawa kan batun Afirka a ranar da yamma.

Ainihin batun Afirka shi ne samun bunkasuwa. Sanin kowa, sabo da kasashe masu ci gaba sun taba yin mulkin mallaka a nahiyar Afirka, shi ya sa suke daukar alhaki kan halin fama da talauci da Afirka ke ciki da kuma taimaka wa Afirka wajen warware batun samun bunkasuwa.

A cikin sanarwar da kungiyar G8 ta bayar bayan taron, an sake jaddada cika alkawarin da suka yi na tallafa wa Afirka yau da shekaru uku da suka gabata a gun taron koli da aka yi a kasar Birtaniya. A shekara ta 2005, shugabannin kungiyar G8 sun taba yin alkawarin kara yawan kudaden taimako da gwamnatocin kasashen za su samar wa Afirka har ninki daya kafin shekara ta 2010 domin ya kai dala biliyan 50 a ko wace shekara.

Kuma wannan shi ne karo na uku da kungiyar G8 ta yi wannan alkawari a jerin shekaru uku da suka gabata.

Amma abin bakin ciki shi ne ko da yake kungiyar ta yi alkawarin da ke iya karfafa zukatan mutane sosai, amma ba ta yi kokarin a zo a gani ba lokacin da take cika alkawarin. Bisa sabuwar kididdigar da kungiyar hadin gwiwa don samun bunkasuwar tattalin arziki ta bayar, an ce, ya zuwa yanzu yawan kudaden taimako da kungiyar G8 ta samar bai kai rubu'i ba bisa wadanda suka yi alkawarin samarwa.

Daina yin kokari wajen cika alkawarin da kungiyar ta yi ya yi illa sosai ga kasashen Afirka kai tsaye wajen cimma burin samun bunkasuwa da aka tsara a shekara ta 2000. A gun taron koli na MDD na shekara ta 2000, shugabannin kasashe daban daban sun tabbatar da buri a fannoni 8, ciki har da ya zuwa shekara ta 2015, za a kau da talauci mai tsanani da Afirka ke fama da shi, da yada ilmi na matakin farko, da kyautata sharudan jiyya da kuma samun dauwamammiyar bunkasuwa a Afirka, ta haka an nuna hanya wajen warware batun Afirka.

1 2