A gun gasar cin kofin Thomas, kungiyar maza ta kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Korea ta kudu da 3 bisa 1, sau uku ne ta rike da zakaran kofin Thomas. Wanda ya fi jawo hankulan 'yan kallo shi ne Lin Dan, a halin da ake ciki yanzu, Lin Dan ya zama matsayin koli a dandalin wasan kwallon badminton na duniya. Amma masu sha'awar wasan kwallon badminton na kasar Sin su kan damu da halinsa saboda wani lokaci a gun babbar gasa, hankalinsa ya kan tashi ba zato ba tsammani. Game da wannan, Lin Dan yana ganin cewa, shiga gasa mai wuya zai kyautata halinsa, ya ce: "A wancen lokaci, na san gasar tana da wuya, amma ba zaben dake gabana, sai na kara yin kokari."
A gun wannan gasa, kungiyar kasar Sin ta samu zakarun kofin Thomas da kofin Uber lami lafiya, wannan ya sake shaida mana cewa, kungiyar wasan kwallon badminton ta kasar Sin tana matsayin koli a duniya. A sa'i daya kuma, 'yan wasan kasar Sin suna kara samun fasahohin gasa. Kafin gasar wasannin Olympic ta Beijing, kungiyar kwallon badminton ta kasar Sin za ta shiga gasanni a jere, haka kuma za ta kara kyautata halinta. (Jamila Zhou) 1 2
|