Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-09 09:40:20    
Kungiyar kwallon badminton ta kasar Sin tana yin namijin kokari domin shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri

A watan Mayu na bana, an yi gasar cin kofin Thomas da kofin Uber tsakanin kungiya kungiya ta wasan kwallon badminton a Jakarta, babban birnin kasar Indonesia. A gun gasar, kungiyoyin maza da mata na kwallon badminton na kasar Sin sun samu zakaru tare.

Gasar cin kofin Thomas da kofin Ubar da ake shiryawa sau daya a duk shekaru biyu gasa ce tsakanin kungiya kungiya mafi matsayin koli a duniya. Makasudin shiga gasar na kungiyar kwallon badminton ta kasar Sin shi ne domin binciken halin da 'yan wasa ke ciki da kuma yin share fage domin gasar wasannin Olympic ta Beijing. Babban malamin koyar da wasa na kungiyar kwallon badminton ta kasar Sin Li Yongbo ya bayyana cewa, bayan wannan gasa, 'yan wasan kungiyarsa suna cike da imani, ya ce:  "Ba ma kawai 'yan wasan kasar Sin sun samu imani ba, har ma suna kara gane kansu da 'yan wasan kasashen duniya, abu mafi muhimmanci shi ne mun tarar da karanci kafin gasar wasannin Olympic kuma muna kara samun imani."

A gun zagaye na karshe na gasar cin kofin Uber, kungiyar kwallon badminton ta mata ta kasar Sin ta lashe kungiyar Indonesia wato kasa mai sauki baki da 3 bisa 0, a karo na shida ne ta ci gaba da samun zakarar kofin Uber. Amma kungiyar kasar Sin ta sha wahala kafin ta ci nasara ta karshe. Shaharariyar 'yar wasan kungiyar kasar Sin Xie Xingfang tana ganin cewa, kamata ya yi ta kara kyautata karfin dace da muhalli, ta ce:  "Kowace gasa horo ne gare mu, yanzu gasar wasannin Olympic tana kara kusantowa, ina fatan zan kara kyautata halina, amma wani lokaci, ban iya dace da muhalli ba cikin sauri."

Xie Xingfang za ta dauki nauyin neman samun lambar zinariya ta mata a gun gasar wasannin Olympic da za a shirya a Beijing, hakikanan abubuwa sun shaida mana cewa, Xie Xingfang za ta warware matsalolin dake gabanta, musamman ma bayan da ta ci hasara. Ban da wannan kuma, sabbin 'yan wasa su ma sun samu fasahohi a cikin gasannin da aka shirya musu. Babban malamin wasa Li Yongbo yana ganin cewa, "A da, a kullum kungiyar kasar Sin ta ci nasara cikin sauki, amma a gun wannan gasa, ta gamu da wahala, duk da haka, kungiyar kasar Sin ta yi namijin kokari, a karshe dai, ta ci nasara, lallai irin wannan horo yana da muhimmanci sosai ga 'yan wasa."

1 2