Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-03 18:08:12    
Wata kyakkyawar yariniya ta kabilar Uygur, wadda ta yi yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a jihar Xinjiang

cri

A ranar 31 ga watan Yuli na shekarar 2001, birnin Beijing ya samu damar shirya wasannin Olympics na shekarar 2008 a gun cikakken taro na kwamitin wasannin Olympics na duniya da aka shirya a birnin Moscow. A lokacin kuma, bisa matsayinta na wata mai rawa ta kungiyar wake-wake da raye-raye ta jihar Xinjiang, Rena ta shiga aikace-aikacen nune-nunen fasahohi da kungiyar wakilai ta birnin Beijing wajen neman damar shirya wasannin Olympics ta shirya a Moscow. Rena ta gaya wa wakilinmu cewa, wancan ne karo na farko da ta yi cudanya sosai da wasannin Olympics, shi ne kuma abin da ya fi kawo mata alfarma a rayuwarta. Ta nasarar da birnin Beijing ya samu wajen shirya wasannin Olympics, Rena tana iya jin wani irin farin ciki daga jama'ar kabilu daban daban na kasar Sin, da jama'ar dukkan duniya, wannan shi ne wasannin Olympics. Ta ce, "A lokacin da birnin Beijing ya samu nasara wajen neman damar shirya wasannin Olympics na shekarar 2008, ina wasan nune-nunen fasahohi a birnin Moscow, lallai wannan ne taimakon da na bayar kan wannan abu mai tsuma jiki, har ma ban iya yi magana a lokacin ba."

Tun bayan da ta soma aiki a shekarar 1992, sai kullum Rena tana aikin raye-raye na kabilar Uygur, kuma kokarin da ta yi, ya haddasa babbar nasara. A shekarar 1998, Rena ta samu lambar daraja ta farko a babbar gasar raye-raye ta jihar Xinjiang, kuma ta samu lambar daraja ta biyu a babbar gasar raye-raye ta dukkan kasar Sin a karo na hudu. Ban da wannan kuma, sau da yawa an lakanta wa mata "ma'aikaci mai ci-gaba".

A ranar 17 ga watan Yuni, an soma yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a garinta na jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur, wannan ne kuma karo na biyu da Rena ta yi cudanya sosai da wasannin Olympics. A ganin Rena, fitilar wasannin Olympics na nuna zaman lafiya, da sada zumunta, da kuma hadin gwiwa. Bayan da ta kawo karshen yawo da fitilar, Rena ta nuna fatan alheri ga wasannin Olympics na Beijing da harsunan Uygur, da Han. Ta ce, "Ni ce Rena Abudu Kelim, na fito ne daga kungiyar wake-wake da raye-raye ta jihar Xinjiang. Ko da yake na kammala yawo da fitilar ba da dadewa ba, amma ba na jin gajiya ko kadan. Ko shakka babu, za mu samu nasara kan wasannin Olympics na shekarar 2008 na Beijing."


1 2