Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-03 18:08:12    
Wata kyakkyawar yariniya ta kabilar Uygur, wadda ta yi yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a jihar Xinjiang

cri

A cikin masu yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing da yawansu ya kai 624 daga jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin, yawancinsu sun fito ne daga kananan kabilu. Ciki kuwa akwai wata kyakkyawar yariniya ta kabilar Uygur, wadda ta fi jawo hankulan mutane, saboda ta yi yawo da fitilar ta wata hanyar Romantic, wato ta yi yawo da fitilar tare da rawa. Wannan yariniya ita ce, Rena Abudu Kelim, wadda ta fito ne daga kungiyar wake-wake da raye-raye ta jihar Xinjiang. Yanzu ga bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana daga jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur.

Dogon jitso, da karamar hula mai launuka iri iri, da kuma raye-raye masu alfarma, su ne tunani mai kyau da Rena Abudu Kelim ta bayar wa mutane a lokacin yawo da fitilar wasannin Olympics. Wannan 'yar kabilar Uygur ta yi amfani da wannan hanyar musamman, don bayyana fatan alhari da zuciya daya ga wasannin Olympics. Rena ta fayyace cewa, raye-rayen da ta yi suna da ma'anar musamman sosai.

"Na yi raye-rayen don gaya wa jama'ar duniya cewa, mu jama'ar jihar Xinjiang muna fatan za ku fahimci jiharmu."

Rena ta gaya wa wakilinmu cewa, ban da maraba da zuwan fitilar wasannin Olympics ta hanyar yin raye-raye na jihar Xinjiang, kuma tana da zuciya daya don maraba da abokanmu daga kasashe daban daban da su zuwa nan kasar Sin, ciki har da jihar Xinjiang. Ta ce, "Sannunku, ni ce Rena Abudu Kelim, wata mai rawa daga kungiyar wake-wake da raye-raye ta jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur, ni ce kuma mai yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing. Ko shakka babu na yi farin ciki sosai, saboda na iya zama wani mai yawo da fitilar."


1 2