Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-02 15:36:58    
Vitamin D yana iya ba da taimako wajen shawo kan sankara

cri

Bisa wani sabon sakamakon nazarin kimiyya da manazarta na kasar Amurka suka bayar, an ce idan jikin dan Adam ya samu isasshen vitamin D, to za a iya rage hadarin kamuwa da sankarar hanji da ta mama.

Manazarta na makarantar San Diego, wani reshe na jami'ar California ta kasar Amurka sun kiyasta cewa, idan an samu isasshen vitamin D, to za a iya rage mutane dubu 250 da ke kamuwa da sankarar hanji da kuma dubu 350 da ke kamuwa da sankarar mama a ko wace shekara, kuma za a iya samun wannan sakamako a bayyane sosai a kasashen da ke arewacin duniya.

Shan hasken rana zai ba da taimako wajen samun vitamin D, sabo da haka manazarta sun yi nazari kan yawan kwanakin samun hasken rana da na samun gajimare na yankuna fiye da 10 ta hanyar yin bincike da tauraron dan Adam, daga baya kuma sun ja jini daga wasu mutanen da ke kasashen domin tabbatar da yawan vitamin D da ke cikin jininsu. Daga bisani kuma sun kwatanta bayanan yawan vitamin D da ke cikin jini da na yawan kwanakin samun hasken rana na kasashe fiye da 170 domin kara yin bincike.


1 2 3