Mataimakin darektan hukumar zirga zirga ta birnin Beijing Mr. Zhou Zhengyu ya bayyana cewa, a yayin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics, tilas ne birnin Beijing ya dauki matakai masu amfani domin sassauta matsi a fannin zirga zirga, wannan kuma ya zama wani misalin kasashen duniya a yayin da suke gudanar da gasar wasannin Olympics. Ya ce,
'Game da biranen da suka shirya gasar wasannin Olympics, ya kasance da babbar matsi daga zirga zirga a yayin da suke gudanar da gasar, haka kuma ya kasance da babbar bukata daga hidimar zirga zirga. Sabo da haka ne, biranen Seoul, da Athens sun dauki matakai domin tabbatar da zirga zirgar gasar wasannin Olympics.'
Mazauniyar birnin Beijing Madam Zheng Jie ta yi imani cewa,
'Wadannan matakai suna da amfani ga birnin Beijing. Ta hakan ne, za a kyautata zirga zirga, haka kuma za a iya kara ingancin iska ta birnin Beijing. A nan gaba ba da dadewa ba za a shirya gasar wasannin Olympics, wadannan matakai za su kara kyautata ingancin iskar Beijing, jama'ar birnin Beijing za su iya more wani kyakkyawan yanayi a lokacin da za a gudanar da gasar wasannin Olympics.'(Danladi) 1 2
|