Ko da bayan shekaru kusan dubu daya, amma ya zuwa yanzu hali mai kyau da kuma gine-ginen gargajiya da aka samu a gidan ibada na Dajuesi sun yi kama da yadda suke zama a can can can da. Yanzang ya kara da cewa,
'Ko da an canza zamanin dauloli, kuma tarihi ya sami sauye-sauye, amma a matsayinsa na abun tarihi na al'adu, gidan ibada na Dajuesi ya nuna karfin rayuwa. Abubuwan da ya yada, wato hikimar mutanen gabashin duniya da karfin zuciya da rashin durkusawa a gaban kome da yin aikin tukuru da jaruntaka da nuna budaddiyar zuciya da kuma kishin zaman lafiya, yana ci gaba da yaduwa, kamar yadda furannin magnolia wato Yulan suke ci gaba da yin toho a gidan ibada na Dajuesi.'
Furannin Yulan sun jawo hankulan mutane sosai a gidan ibada na Dajuesi, su ma alamar wannan gidan ibada. A ko wane lokacin bazara, a kan yi bikin al'adun furen Yulan a gidan ibada na Dajuesi. Ba gidan ibada na Dajuesi kawai ake iya samun furannin Yulan ba, amma don me bikin al'adun furen Yulan da a kan shirya a nan ya shahara sosai? Zhao Heng, babban edita na wani kamfanin wallafawa na Beijing ya dade yana nazarin tarihi da al'adu na gidan ibada na Dajuesi, ya yi karin bayani da cewa, tsawon shekarun babban icen furen Yulan a gidan ibada na Dajuesi ya wuce dari 3. Ya ce,
'Shugaban gidan ibada na Dajuesi ya kaurar da wannan icen furen Yulan daga babban dutsen Lushan, shi ya sa shi furen Yulan ne na kudancin kasar Sin. Yau da shekaru dari 2 ko fiye aka kaurar da shi zuwa wannan gidan ibada. Ya kan yi toho a misalin ko wane watan Afrilu bisa kalandar wata ta kasar Sin. A da wannan icen furen Yulan ba shi da tsayi sosai, amma yana da furanni da yawa kuma masu kyan gani sosai, shi ya sa a kan rubuta rubutattun wakoki kan wannan icen furen Yulan.'
A shekarar 1997, an kebe wani wuri da ke cikin gidan ibada na Dajuesi da ya zama wurin shan shayi. An kuma kebe dakunan shan shayi a ko ina na gidan ibada na Dajuesi, sa'an nan kuma, an kafa wani dakin cin abinci. Ban da wannan kuma, an yi kwaskwarima kan dakunan mabiyan addinin Buddha da ba a ci gaba da yin amfani da su a wannan gidan ibada da su zama dakunan kwana da kuma fitattun dakunan kwana. Ban da wannan kuma, an gina dakunan taro da sauran gine-ginen nishadi a gidan ibada na Dajuesi. Kazalika kuma, ana ajiye kujeru da teburorin shan shayi a lambun gidan ibadan. Kamshin shayi da na furanni da kuma tsoffin itatuwa sun zama halin musamman na gidan ibada na Dajuesi.
Yanzu ana bude kofar gidan ibada na Dajuesi ga matafiya a duk shekara. Lokacin bazara lokaci ne da furannin Yulan suka yi toho. Masu yawon shakatawa su kan ji farin ciki sosai saboda kallon kyan ganin furanni. Daya daga cikinsu wato Jia Ming ya gaya mana cewa,
'Gidan ibada na Dajuesi, wani wuri ne mai ban sha'awa, kuma an yi tsit a wajen. Mu kan kawo nan ziyara sau da dama a ko wace shekara. Ina sha'awar rafi da itatuwa a wannan gidan ibada.' 1 2
|