Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-01 15:10:45    
Gidan ibada na Dajuesi a Beijing

cri

Birnin Beijing, wani babban birni ne mai wadata kuma mai cike da mutane. In kuna so ku sami wani wurin da aka yi tsit a wajen, to, akwai wurare masu kyau da yawa da mutane suka iya kwantar da hankulansu a Beijing. Yau ma bari mu je yammacin Beijing domin kai ziyara ga wani gidan ibada mai tsawon shekaru kusan dubu, sunansa shi ne Dajuesi.

In kun tashi daga shahararren fadar bazara wato Yiheyuan da ke yammacin Beijing, kun dauke minti goma ko fiye kawai cikin mota, sai za ku isa gidan ibada na Dajuesi da ke babban dutsen Xishan a nan Beijing. An gina gidan ibada na Dajuesi a zamanin daular Liao, wato a shekarar 1068, tsawon shekarunsa ya kai kusan dubu guda. Saboba akwai wani rafin da ke gangarowa a gidan ibadan, shi ya sa a kan kira shi gidan ibada na Qingshuiyuan. Ana iya ganin abubuwan da ke nuna tsawon dubban shekaru a ko ina na wannan gidan ibada, kamar duwatsun sassaka da gine-gine da kuma allunan rubuce-rubuce. An yi kama da tarihi ya sanya dukkan ciyayi da itatuwa da ke cikin gidan ibada na Dajuesi su sami basira. Har ma an mai da hankali kan wurin da wannan gidan ibada yake. Yanzang, wani shehun malami na hadaddiyar kungiyar addinin Buddha ta kasar Sin kuma babban mashawarci mai kula da al'adun addinin Buddha na gidan ibada na Dajuesi ya yi mana bayani da cewa,

'Wannan gidan ibada na fuskantar gabas, ta haka a ko wace rana da safe, hasken rana na farko da ya gamu ya iya kawo wa al'ummomin kasar kyakkyawan fata. Yawancin gine-ginen gargajiya na kasar Sin na fuskantar kudu, don haka gidan ibada na Dajuesi ya sha bamban da saura sosai, ya kuma nuna cewa, al'adun kasar Sin na kunshe da bangarori daban daban cikin jituwa, haka kuma, kabilu da yawa suna nuna wa juna amincewa ta fuskar al'adu.'


1 2