Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-30 15:14:30    
Makamashin hasken rana da ake amfani da shi cikin zaman yau da kullum na jama'a 'yan kabilar Tibet

cri

Fararen hula 'yan kabilar Tibet suna ta kara sayen kayayyakin da ake amfani da su da makamashin hasken rana cikin zamansu na yau da kullam, wannan kuma ya kawo musu moriya wajen kimiyya da fasaha. Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin jihar Tibet ta mai da muhimmanci sosai kan aikin sarrafa makamashin hasken rana, ta kara ware kudi da yawa domin wannan aiki, musamman ma domin biciken kimiyya. Yanzu fararen hula sun fi sayen murhu da na'urar dumama ruwa wadanda suke amfani da su da makamashin hasken rana cikin gidajensu. Mr. Tsering Norbu, saketaren ofishin gwajin kimiyya na cibiyar binciken makamashi ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana a kan wannan batu cewa, cibiyar za ta ci gaba da yin kokari domin binciken fasahar yin amfani da makamashin hasken rana, ya ce,

"An kafa fitilun ba da haske ga filayen ciyayi da hanyoyi wadanda ake aiki da su da makamashin hasken rana, wadanda kuma aka sarrafa su da haske. In dare ya yi, gari ya yi duhu, sai kuma fitilu su fara ba da haske su da kansu. Ko kwanaki 5 ba a samu hasken rana a birnin Lhasa ba ana iya samar da wutar lantarki. Ban da wannan kuma a lokacin sanyi, mukan yi amfani da na'urar dumama ruwa domin ba da iska mai zafi cikin ofis. A lokacin zafi kuma ba a bukatar iska mai zafi, sabo da haka sai a yi amfani da makamashin hasken rana domin samar da ruwan zafi ga unguwannin mazaunan birnin, har ma ana iya shan irin wannan ruwa mai zafi."

Yanzu a jihar Tibet da akwai manoma da makiyaya wadanda yawansu ya kai kusan dubu 300 wadanda kuma suke samun moriya ta hanyar yin amfani da kayayyaki masu aiki da makamashin hasken rana.


1 2