Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-30 15:14:30    
Makamashin hasken rana da ake amfani da shi cikin zaman yau da kullum na jama'a 'yan kabilar Tibet

cri

Ana kiran jihar Tibet mai cin gashin kai ta kasar Sin da sunan "wurin da ya fi kusa da rana" sabo da tsayinta daga leburin teku. Yanzu mutane 'yan kabilar Tibet suna ta kara yin amfani da makamashin hasken rana cikin zaman yau da kullum, dafa ruwan sha ko yin wanka ta hanyar yin amfani da na'urar dumama ruwa, wannan ya riga ya zama wata hanyar zamani da dimbin iyalan kabilar Tibet ke bi cikin zaman rayuwarsu. To jama'a masu sauraro, cikin shirinmu na yau za mu yi muku bayani kan yadda ake yin amfani da makamashin hasken rana mai tsabta da kuma yayata shi a jihar Tibet mai cin gashin kai.

Mr. Tsomo, dan kabilar Tibet wanda ya fito daga birnin Lhasa na jihar Tibet ya bayyana cewa,

"Muna yin amfani da makamashin hasken rana a gidajenmu domin wanke kayan lambu da dafa abinci da wanka cikin sauki, da rana mun zuba ruwan sanyi a cikin tanki, da dare kuma za mu iya samun ruwan zafi, amma a da mukan dafa ruwa da kirare, shi ya sa akan cika wuri da hayaki a cikin dakuna."

Bisa matsayinsa na wani sabon makamashi, makamashin hasken rana yana da kyau wajen kiyaye muhalli da sake samun shi idan an kwatanta shi da na makamashin gargajiya. Jihar Tibet ta kasar Sin ta kama matsayi mai rinjaye wajen samun irin wannan makamashi mai inganci. Mr. Wang Haijiang, mataimakin mai yin bincike da nazari na cibiyar binciken makamashi ta jihar Tibet ya bayyana cewa,

"Alabarkatun da muke ambata a kai yana da ma'ana a fannoni 2 wato daya shi ne, yawan sa'o'in da ake samun hasken rana a kowace rana, dayar kuma shi ne karfin hasken rana. Matsakaicin yawan sa'o'in da ake iya samun hasken rana a jihar Tibet ya kai kusan sa'o'i 3000 a kowace rana, wato ya ninka sau 2 ko fiye bisa na sauran wuraren da ke cikin kasar Sin wadanda yawan digirinsu daya ne kan layin taswirar latitude na duniya, babu shakka a kan wannan batu. Sabo da haka jihar Tibet tana da albarkatun makamashin hasken rana sosai, kuma ta zama wurin da ya dace wajen bunkasa harkokin makamashin hasken rana."


1 2