Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-30 15:08:42    
Ana raya sansanin noman kayayyakin lambu a kasar Sin cikin daidaici

cri

Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima da bude wa kasashen waje kofa, ta bunkasa harkokin noman kayayyakin lambu cikin sauri sosai, yawan kayayyakin lambun da ta samu ya wuce tan miliyan 580 a shekarar bara, sa'an nan kuma kasar Sin ta kai matsayi na farko a duniya wajen sayar da kayayyakin lambu zuwa kasashen waje. Da aka tabo magana a kan kayayyakin lambu na kasar Sin, a kan nuna yabo cewa, birni mai suna Shouguang na lardin Shandong muhimmin sansanin noman kayayyakin lambu ne a kasar Sin.

Birnin Shouguang yana tsakiyar lardin Shandong, yana da albarkatun kasa masu yawa da hanyoyin tafiye-tafiye cikin sauki sosai. Yau da shekaru 20 da suka wuce, bisa binciken da ya yi, Malam Wang Leyi, dagacin wani kauye mai suna Sanyuanzhu na birnin Shouguang ya fara gina dakunan leda na noman kayayyakin lambu wadanda ake dumama su a yanayin dari, ta haka aka fara samun kayayyakin lambu iri daban daban a birnin Shuoguang cikin dukkan shekara baki daya. Musamman ma a cikin shekarun nan da suka wuce, yawan kayayyakin lambun da birnin ke sayarwa zuwa kasashen waje ya yi ta karuwa. Da Malam Wang ya tabo magana a kan wannan, sai ya ce, sun taba shan wahala wajen sayar da kayayyakin lambu zuwa kasashen waje. Ya kara da cewa, "mun fara sayar da kayayyakin lambu zuwa kasashen waje ne a shekarar 2000, amma a wancan lokaci, ba mu noma kayayyakin lambu cikin daidaici, don haka ba mu iya sayar da kayayyakin lambu zuwa kasashen waje bisa shirin da muka tsara. Alal misali, a da tumatir kawai muke sayarwa zuwa kasar Rasha. Idan ingancin samfurin tumatir da muke kai wa kasar bai kai ma'auninta ba, to, ba za mu iya sayar da shi zuwa kasar kamar yadda ya kamata ba."


1 2 3