Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-26 19:02:42    
Kasar Sin ta daidaita yawan kasafin kudi domin sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kudi na Sichuan

cri

Haka kuma, domin wannan asusun sake raya yankuna masu fama da bala'in girgirzar kasa yana bukatar kudade masu dimbin yawa, dole ne gwamnatin kasar Sin ta tattara su daga fannoni daban daban. Bisa shirin da aka tsara, za a kebe kudin Sin yuan biliyan 60 daga asusun tabbatar da daidaita kasafin kudi. Sannan kuma, za a tattara sauran kudade daga harajin da ake bugawa kan motocin da ake saya da cacar kuri'a da dai sauransu. Mr. Xie ya ce, "Za a tattara wadannan kudade ne ta hanyoyi daban daban. Bayan da aka kafa wani asusu, za a iya yin amfani da su tare domin ayyukan sake raya yankuna masu fama da bala'in. A shekarar da muke ciki, yawan kudaden da gwamnatin tsakiya ta ware domin sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na Wenchuan ya yi dimbin yawa. A nan gaba, gwamnatin tsakiya za ta ci gaba da kebe wa wannan asusu karin kudade bisa halin da ake ciki kan yadda ake sake raya yankunan da yadda ake tattara kudade."

Lokacin da ya tabo magana kan yadda za a yi amfani da kudaden wannan asusu, Mr. Xie ya ce, za a yi amfani da wadannan kudade domin gina wuraren kwana na fararun hula da makarantu da asibitoci da kuma ayyukan yau da kullum na wutar lantarki da na samar da ruwan sha. A waje daya kuma, za a yi amfani da su domin farfado da aikin gona da masana'antu da kasuwanci da aikin rigakafin aukuwar sauran bala'u daga indallahi a yankuna masu fama da bala'in. Game da yadda za a yi amfani da wadannan kudade, Mr. Xie ya kara da cewa, "Za a tsaya kan matsayin bin manufar mai da dan Adam a gaban kome lokacin da ake amfani da wadannan kudade. Wato da farko dai za a yi amfani da wadannan kudade domin tabbatar da zaman rayuwar yau da kullum da ayyukan yau da kullum da jama'a masu fama da bala'in suke bukata cikin gaggawa."


1 2