A ran 26 ga wata, a gun taron zaunannen kwamitin majalisar dokokin kasar Sin, wato majalisar koli ta ikon mulkin kasar Sin, an zartas da shirin daidaita kasafin kudi da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta gabatar. Sakamakon haka, tun daga shekarar da muke ciki, gwamnatin kasar Sin za ta kebe kasafin kudi daga baitulmali domin kafa wani asusun sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na Wenchuan na lardin Sichuan. Yawan kudin da ta kebe wa wannan asusu a cikin shekarar da muke ciki ya kai kudin Sin yuan biliyan 70, wato kimanin dalar Amurka biliyan 10. Yanzu ga wani bayani game da dalilin da ya sa aka kafa wannan asusu, kuma yadda ake tattaara kudi da kuma yadda ake amfani da shi.
Yanzu an riga an shiga sabon matakin fama da bala'in girgizar kasa da ya auku a gundumar Wenchuna ta lardin Sichuan. Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta riga ta tsara shirin sake raya yankuna masu fama da bala'in. Ta kuma tsai da kudurin daidaita kasafin kudin da take kashewa. Sabo da haka, a ran 24 ga wata, Mr. Xie Xuren, ministan kudi na kasar Sin ya gabatar da wannan kuduri ga taron zaunannen kwamitin majalisar dokokin kasar Sin. A gun taron, Mr. Xie ya ce, "Daidaita kasafin kudin da gwamnatin tsakiya take shiryawa a shekara ta 2008, da kuma kebe wasu kudade domin sake raya yankuna masu fama da bala'i domin maido da odar aikin kawo albarka da zaman rayuwar jama'a a yankunan kamar yadda ya kamata da ciyar da tattalin arziki da zaman al'umma na yankunan gaba. A shekara ta 2006, gwamnatin kasar Sin ta kafa asusun tabbatar da daidaita kasafin kudi. Ya zuwa yanzu, yawan kudaden da ba a yi amfani da su ba ya kai kudin Sin yuan biliyan 103.2. Za mu iya yin amfani da su. Idan mun kebe wasu daga cikinsu domin sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa, ba za a yi mummunar asiri ga aikin yin amfani da kasafin kudi na yau da kullum ba, kuma za a biya bukatun da ake nema a shekarar da muke ciki waje sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa."
1 2
|