Ya zuwa yanzu, birnin Beijing ya kammala ayyukan yin kwaskwarima kan kayayyakin tarihi da kiyaye su cikin shekaru 8 da suka wuce. Amma za a ci gaba da yin aikin nan ba tare da kasala ba.
Mr Kong Fanzhi, shugaban hukumar kiyaye kayayyakin tarihi na al'adu na birnin Beijing ya bayyana cewa, A nan gaba, za mu ci gaba da mai da muhimmanci ga yin kwaskwarima kan kayayyakin tarihi da kuma kara karfin aikin. Don ci gaba da aiwatar da aikin kiyaye kayayyakin tarihi bayan wasannin Olimpic na birnin Beijing, gwamnatin birnin Beijing ya tsai da cewa, daga shekarar 2008 zuwa shekarar 2015, birnin Beijing zai aiwatar da shirin dogon lokaci da na matsakaicin lokaci na yi wa kayayyakin tarihi kwaskwarima da kiyaye su. Kuma a kowace shekara za ta ware kudin musamman da yawansu ya kai miliyan 150 don kiyaye kayayyakin tarihi.(Halima) 1 2
|