Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-25 19:05:38    
Aikin kiyaye kayayyakin tarihi da birnin Beijing ya yi cikin shekaru 8 ya kammala lami lafiya

cri

Kwanan nan, birnin Beijing ya kammala aikin kiyaye kayayyakin tarihi da ya yi cikin shekaru 8 lami lafiya. A cikin shekaru 8 da suka wuce, yawan kudaden da gwamnatin birnin Beijing ta ware don kiyaye da kuma yin kwaskwarima kan kayayyakin tarihi ya kai kudin Sin Yuan miliyan 930, saboda haka an sami sakamako mai kyau a bayyane.

Birnin Beijing yana da tarihin da yawan shekarunsa ya wuce dubu 3 ko fiye wajen gina shi, tare da tarihin kafa hedkwatar kasa da yawan shekarunsa ya kai 800 ko fiye, shi ne mashahurin birnin da ke da tarihi da al'adu a duniya. Ban da gine-ginen tarihi na duniya da suka kunshe da fadar sarakuna wato "Gugong" da dandalin nuna bikin girmamawa ga sararin samaniya wato "Tiantan" da babbar ganuwa , birnin Beijing shi ma yana da lambunan shan iska na sarakuna da yawa da gine-ginen addinai da gidajen jama'a da sauran gine-ginen tarihi da ba a iya kaurar da su ba , kuma yawansu ya kai 3500 ko fiye. Wani mashahurin kwararren kayayyakin tarihi na kasar Sin Mr Xu Pingfang ya bayyana cewa, game da samun bunkasuwar birnin Beijing cikin dogon lokaci, kiyaye kayayyakin tarihi na da ma'ana mai muhimmanci sosai, ya ce,biranen kasar Sin na zamani aru aru suna da dogon tarihi, wanda ya yi daidai da lokacin da kasar Sin ta sami wayewar kai. Biranen kasar Sin na zamani aru aru sun yi ta samun bunkasuwa. A duk tsawon lokacin da suka samu bunkasuwar, sun samu hanyoyin musamman da yawa da suka bi da kuma lokutai iri iri na samun bunkasuwa da suke ciki , sun yi banbanci da na kasashen Turai. An gina tsohon birnin Beijing a daular Yuan da daular Ming da daular Qing , ana iya cewa, birnin shi ne birni mafi kyau da aka gina shi a zamani aru aru kuma aka raya shi ta hanyar gargajiya. Gine-ginen da ke nuna wayewar kai ta kasar Sin rabinsu suna kasancewa cikin tsoffin biranen zamani aru aru, saboda haka tsoffin biracne na zamani aru aru na kasar Sin su ne kayayyakin tarihi na al'adu mafi muhimmanci sosai na kasar Sin.

Daga shekarar 2000, birnin Beijing ya soma yin kwaskwarima kan kayayyakin tarihi da ba a iya kaurar da su ba da kuma kiyaye su. A shekarar 2002, birnin Beijing ya soma aiwatar da shirin kiyaye yankunan kiyaye kayayyakin tarihi na al'adu na tsohon birnin Beijing cikin shekaru 25 da shirin kiyaye shahararen birnin Beijing da ke da tarihi da al'adu , sa'anan kuma ya yi wa gine-ginen tarihi fiye da 100 kwaskwarima. Shugaban hukumar kiyaye kayayyakin tarihi ta birnin Beijing Mr Kong Fanzhi ya bayyana cewa, a wannan gami, an mai da muhimmanci ga yin kwaskwarima kan gine-ginen tarihi na duniya guda 6, da farko an kara ingancin gine-ginen "Gugong" da muhallin da ke kewayensa, sa'anan kuma an kara ingancin gine-ginen "Tiantan", ayyuka da yawa gare mu su ne ayyukan yi wa muhallin da ke kewayen wadannan gine-ginen tarihi kwaskwarima. Sa'anan kuma an yi gyare-gyare kan Summer Palace wato "Yiheyuan" da kaburbura 13 na daular Ming , wato "Shisanling".

Daga shekarar 2003, gwamnatin birnin Beijing ta soma aiwatar da shirin shekaru biyar na kiyaye kayayyakin tarihi na wasannin Olimpic da ke dace da 'yan Adam. Yawan kudin da ya ware ya kai kudin Sin Yuan miliyan 600. Wani jami'in kula da kayayyakin tarihi na birnin Beijing Mr Wang Yuwei ya bayyana cewa, aikin yin kwaskwarima kan haikalin Confisius da Guozijian ya kasa fannoni biyu, na farko, kaurar da wasu sassan da ke zama a ciki, na biyu, an kara girman matakan yin gyare-gyare.

1 2